Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na girki adon mata.
Abubuwan da Uwargida ya kamata ta tanada:
Fulawa, kwai, madara, Fankek in an ce fankek ba a nufi fanke ba wato (bones), ana nufin wani abu kamar wainar fulawa ko kuma wainar kwai haka yake.
 Yadda Uwargida za ki hada
Da farko uwargida za ki samo roba haka sannan ki kawo fulawa kamar kofi biyu, sai ki fasa kwan guda biyu, sannan ki kawo Madara ki zuba kamar babban cokali uku sai ki juya shi sosai da injin da ake hada kek wato (mider), idan ya juyu sosai ya kwabo sai ki kawo fiyin fan dinki, ki dora shi a wuta idan so sumu ne ki samu wanda ba sai kin sa masa mai ba saboda kamar kashi ake masa idan kuma ba ki samu ba sai ki yi na non-stick fraying pan din ki rika sa masa mai kadan za ki rika shafawa sannan sai ki fara zubawa kina soyawa ko kuma na ce kasawa haka za ki yi har ki gama, bayan kin gama soyawa za ki jera shi a tire haka, sannan sai ki kawo maple syrup din ki, ki barbada akwai idan ba ki da shi za ki iya zuba zuma sannan sai ki yanki bota karama haka ki saka a saman su kamar kwalliya haka.
Wani hadin daban:
Abin da uwargida za ta tanada:
Fulawa, kwai, Madara, Food colouring, Yadda za ki hada
Da farko ki saka fulawa kofi biyu, sannan ki fasa kwai sai ki zuba Madara babban cokali uku, sai ki juya shi sosai da mider, sai ki saka a kwano guda, hudu sannan ki saka food coloring kalar ruwan kwai, shudi mai haska, da shudi mai duhu, sai ruwan goro sai ki juya kowannan su sosai, sannan sai ki fara gasa shi kamar yadda wancan yake, ki jera shi a tire ki dan masa kwalliya kamar de wancan hadin.