Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
Ga Abubuwa da Uwargida za ta tanada
Gyada, gishiri, kwai, suga, filaibo, madara ta gari, fulawa, da mai
Da farko za ki samu gyadarki mai bargo wato wacce ba’a murje bayanta ba jan jikinta, sai ki zuba ta a wata roba haka, ki zuba gishirinki kamar babban cokali biyu sannan ki samu ruwa mai zafi ki zuba akan ta ki barshi ya yi kamar minti biyar haka sai ki zuba ta a Kwando, saboda ta tsane ruwan ki barta ruwan ya tsane so sai ki zuba ta a tire ki shanya ta ta bushe, idan ta bushe sai ki samu wani kwano daban ki fasa kwan a ciki sai ki zuba suga kamar kofi daya zuwa biyu yadda zai isa, sannan ki zuba filaibo babban cokali daya ki kada shi sosai ya kadu ki ajiye shi a gefe.
Sannan ki samo wani kwanon ki zuba kofi daya na fulawa ki zuba madarar gari kamar babban cokali uku a cikin fulawar, sai gishiri babban cokali daya ki gauraya fulawar ki ajiye ta a gefe, sannan ki dakko wannan kwan da kika hada ki barbada shi a cikin gyadar sai ki juya ta duka gyadar ta samu kwan sannan ki kawo filawar da kika hada ki zuba akan gyadar kina gauraya ta haka za ki yi har ta kare za ki ga jikin gyadar ya zama fari, ko kuma ki barbada kwan kamar cokali biyu ki gauraya ki debi fulawar kadan haka ki barbada ki gauraya za ki iya yin haka kina barbada kwai kadan kina sa filawa kadan har su kare duk daya ne da wancan idan ta zama fara wato filawar ta rufe gyadar sai ki dora mai a wuta ki fara suya.