Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda uwargida za ta hada miyar Uwaidu:
Abubuwan da uwargida za ki tanada
Nama, uwaidu, tattasai, tumatur, kayan yaji, daddawa, alayyahu, manja, magi, gishiri, kori, albasa.
Da farko uwargida za ki tafasa naman ki, na rago ne ko na shanu ko kuwa na kaza, idan kuma hada su za ki yi kamar na rago da na kaza duk za ki iya, sai ki zuba su a tukunya ki wanke su, sannan ki kawo gishiri da dan magi da kori da albasa ki zuba ki dora tafasarsa, idan ya yi daidai yadda kike bukata sai ki sauke shi ki zuba mai a tukunyar da za ki yi miyar.
Sannan sai ki kwashe ki soya shi, idan ya soyu sai ki kawo kayan miyarki tattasai da tumatur da taruhu idan kina so wanda dama kin jajjaga su ki zuba ki zuba yankakkiyar albasarki sannan ki kawo dakakkiyar daddawa ki zuba, ki dan soya su sama-sama sai ki kawo ruwan tafasar naman ki zuba, ki zuba magi, gishiri, kayan yaji, kori ki juya su, ki rufe kibar shi ya tafasa.
Daga nan sai ki kawo uwaido ki zuba wanda dama kin wanke shi, kin gyara shi kuma kin tafasa shi da ‘yar kanwa ki zuba shi, ki barshi ya dan dahu, sannan ki kawo alayyahu wanda shi kin gyara shi kin kuma yanka shi ki zuba ki dan bar shi ya dahu. Shi kenan kin kammala.
Gaskiya miyar ta hadu ga kyau ga dadi, kuma za ki iya ci da tuwon samo, sakwara da dai sauransu. A ci dadi lafiya