ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Uwargida Za Ta Hada Miyar Uwaidu

by Bilkisu Tijjani
2 years ago
Miyar

Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.

A yau shafin na mu zai koya muku yadda uwargida za ta hada miyar Uwaidu:

Abubuwan da uwargida za ki tanada

ADVERTISEMENT

Nama, uwaidu, tattasai, tumatur, kayan yaji, daddawa, alayyahu, manja, magi, gishiri, kori, albasa.

Da farko uwargida za ki tafasa naman ki, na rago ne ko na shanu ko kuwa na kaza, idan kuma hada su za ki yi kamar na rago da na kaza duk za ki iya, sai ki zuba su a tukunya ki wanke su, sannan ki kawo gishiri da dan magi da kori da albasa ki zuba ki dora tafasarsa, idan ya yi daidai yadda kike bukata sai ki sauke shi ki zuba mai a tukunyar da za ki yi miyar.

LABARAI MASU NASABA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

Sannan sai ki kwashe ki soya shi, idan ya soyu sai ki kawo kayan miyarki tattasai da tumatur da taruhu idan kina so wanda dama kin jajjaga su ki zuba ki zuba yankakkiyar albasarki sannan ki kawo dakakkiyar daddawa ki zuba, ki dan soya su sama-sama sai ki kawo ruwan tafasar naman ki zuba, ki zuba magi, gishiri, kayan yaji, kori ki juya su, ki rufe kibar shi ya tafasa.

Daga nan sai ki kawo uwaido ki zuba wanda dama kin wanke shi, kin gyara shi kuma kin tafasa shi da ‘yar kanwa ki zuba shi, ki barshi ya dan dahu, sannan ki kawo alayyahu wanda shi kin gyara shi kin kuma yanka shi ki zuba ki dan bar shi ya dahu. Shi kenan kin kammala.

Gaskiya miyar ta hadu ga kyau ga dadi, kuma za ki iya ci da tuwon samo, sakwara da dai sauransu. A ci dadi lafiya

Miyar
Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
Girke-Girke

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

September 5, 2026
Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
Girke-Girke

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

August 29, 2026
Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
Girke-Girke

Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice

August 29, 2026
Next Post
Rana Ta 3: Duk Da Dokar Hana Fita Masu Zanga-zanga Sun Fito A Kano

Rana Ta 3: Duk Da Dokar Hana Fita Masu Zanga-zanga Sun Fito A Kano

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

September 12, 2026
jam'iyyu

An Buƙaci Ƴan Takara Su Sanya Tsare-tsaren Yaƙi Da Ɗumamar Yanayi A Jaddawalin Kamfen Ɗinsu

September 12, 2026
Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Amince Da Tsawaita Takunkuman Sudan Na Gajeren Lokaci

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Amince Da Tsawaita Takunkuman Sudan Na Gajeren Lokaci

September 12, 2026
Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

September 12, 2026
2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026
Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.