Wanda aka wakilta ya bayar da auren wata sabuwar amarya ana zarginsa da sace sadakin amaryar, jim kadan kafin a daura auren a cikin wani Masallaci da ke a unguwar Kurna a karamar hukumar Dala a Jihar Kano.
An ruwaito cewa, wadanda suka halarci daura auren, an bar su curko-curko a cikin Masallacin suna jiran a daura auren, amma kuma abin mamaki, sadakin ya yi batan dabo.
- Sakon Sallah: Ina Aiki Dare Da Rana Don Ceto Nijeriya -Tinubu
- NIS Ta Yi Wa Jami’anta 7000 Karin Girma
Wani mazaunin unguwar ta Kurna, Sunusi Dan Mamman, ya bayyana cewa bayan an bata tsawon lokaci mahalarta auren suka yanke shawarar bincika Masallacin da nufin neman sadakin.
Ya sanar da cewa a yayin da suke binciken ne sai suka gano sadakin a aljihun waliyin amaryar, inda waliyin ya bayyana cewa bai san lokacin da sadakin ya shiga aljihunsa ba.
A cewarsa, bayan an gano sadakin an kori waliyin daga cikin Masallacin ganin cewa bai cancanci ya zama wakiliyin amaryar ba, inda aka wakilta wani kaninsa ya yi wakilcin auren.
Majiya ta ce ba ta da wata masaniya kan hakan domin bayan an daura auren, ba a saki ganin waliyin a wajen daurin auren ba.