• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

by Sulaiman and CGTN Hausa
10 months ago
in Daga Kasar Sin
0
wang lili
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kafin horaswar kungiyar wasan kwallon kwando ta mata mai mutane 3 ta kasar Sin a yammacin ranar farkon watan Yunin bana, Wang Lili wadda ta zo filin wasa a karon farko bayan tsawon watanni fiye da 8 rabuwarta da filin wasa ta ce, kafin horaswar, ta tuna ta kiyaye kafar hagu mai dauke rauni a cikin mafarkinta. A cikin zuciyarta, tana jin tsoron sake jin rauni a kafar, don haka tana ganin kafar a cikin mafarkinta.

A birnin Chengdu, Wang Lili ta karbi kofin lambar yabo ta ’yar wasa mafi hazaka wato MVP ta wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 na kakar da ta gabata da hukumar hadin gwiwar wasan kwallon kwando ta duniya wato FIBA ta gudanar. Amma ba ta koma filin wasa ba. Lokacin da take zaune a gefen filin wasan, ana iya ganin alamar rauni a kafarta ta hagu. A watan Satumba na shekarar bara, ta kara jin rauni a kafarta karo na biyu.

  • Huldar Abotar Dindindin Tsakanin Sin Da Kazakhstan Na Samun Ci Gaba Zuwa Sabon Mataki
  • Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta

A yayin wasan karshe na gasar shekara-shekara ta wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 na hukumar FIBA na kakar shekarar 2023, wato wasan dake tsakanin kungiyar Sin da ta Faransa, Wang Lili ta ji rauni domin ta fadi kasa a gasar. A sakamakon hakan, jijiyar da ta hada kashi biyu wadda ta gurde a shekarar 2016 ta sake jin rauni. A lokacin, akwai sauran watanni 10 kawai kafin a bude gasar wasannin Olympics ta Paris.

Wang Lili ta bayyana cewa, tun daga lokacin da ta sake jin rauni a kafarta, ta fara yin kidayar lokacin da ta samu sauki da koma filin wasa. Ta ce, wasu lokuta tana ganin watakila ba za ta shiga filin wasan gasar wasannin Olympics a karo na biyu ba.

wang lili
•Wang Lili ta buga wasan a wasan kusa da kusan karshe na gasar cin kofin duniya ta shekarar 2023

Wang Lili ta ce, lokacin warkewa daga rashin lafiya bai yi daidai da sauran ’yan wasa ba, domin ta samu rauni kan wuri daya sau biyu, kuma an sake yin aikin tiyata a kafar. Likita ya ce, akwai bambanci a kafar bisa na tiyatar da aka yi a karo na farko, kana shekarunta ya yi yawa, ba kamar na matasa ba, akwai wuya yiwuwar samun farfadowa cikin sauri.

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Wang Lili mai shekaru 31 da haihuwa ita ce ’yar wasa mafi yawan shekaru a cikin kungiyar wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 ta kasar Sin a halin yanzu. Ta fito ne daga kungiyar wasan kwallon kwandon mata ta jami’ar Peking, ta buga wasa a gasar wasan kwallon kwandon mata ta kasar Sin wato WCBA a kakar shekarar 2014 zuwa 2015. Bayan hakan, ta taba shiga kungiyar wasan kwallon kwandon mata ta kasar Sin sau da yawa, amma ba ta zama ’yar wasa mafi muhimmanci a cikin kungiyar ba. Har zuwa gasar wasannin Olympics ta Tokyo da aka gudanar a shekarar 2021, ita da abokan wasa na kungiyar wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 ta kasar Sin sun samu lambar tagulla. Wang Lili tana sanya rigar wasa mai lamba 23, kuma tana da kwarewa sosai a buga wasa, don haka masu sha’awar wasan suna kiran ta da suna “Jordan mace ta kasar Sin”.

Bayan hakan, kungiyar ta ci gaba da samun lambobin yabo masu yawa. A shekarar 2022, kungiyar ta samu lambar yabo ta tagulla a gasar cin kofin duniya, kuma ta zama zakara a gasar cin kofin Asiya, Wang Lili ta zama ’yar wasa mafi hazaka wato MVP a wasan. A kasar Sin, Wang Lili ta taba samun maki 60 a cikin wasa daya, don haka ta zama ‘yar wasa ta biyu da ta samu maki 60 a cikin wasa daya a gasar WCBA. A shekarar 2023, Wang Lili ta samu lambobin yabo na MVP sau da dama, dukkan ’yan wasan da kungiyoyin wasan suna mai da hankali kan wannan ’yar wasa mai lamba 23 ta kasar Sin.

wang lili
•Wang Lili da abokan wasanta a gun gasar cin kofin duniya ta shekarar 2023

Amma bayan gasar cin kofin duniya ta shekarar 2023, kungiyarta da ita sun tinkari kalubale. Kungiyarta tana da burin zama matsayi na uku na gaba, amma ba ta cimma hakan ba. A lokacin, Wang Lili ta ji rashin dadi sosai, amma a matsayin ’yar wasa, ta samu farfadowa bayan wasu kwanaki. Amma ta samu babban rauni. Da farko dai, Wang Lili ta kasa fahimtar wannan yanayi, a kullm tana tambayar kanta.

Ko da yake irin wannan rauni ba zai kawo karshen rayuwar ’yar wasa ba, amma ana bukatar dogon lokaci na samun sauki, hakika za a kawo sauyi ga shirin yin horaswa, har ma ga makomar ’yar wasan. A sa’i daya kuma, abokan wasan kungiyarta da ’yan wasan sauran kungiyoyin wasa, suna kiyaye yin kokarin samun ci gaba, gasa ba ta tsaya domin ita ba, wasanni ba za su jira kowa ba.

wang lili
•Wang Lili ta kara yin kuzari wajen samun sauki da neman komawa filin wasa cikin sauri

Wang Lili ta bayyana cewa, bayan da aka yi mata aikin tiyata, ta fuskanci mawuyacin hali, domin ba ta iya tsalle ko gudu ba, har ma ba ta iya yin tafiya cikin sauri ba. Ta ce, idan ba ta karfafa wa kanta gwiwa ba, yana yiwuwa ba za ta iya daidaita yanayin ba.

A lokacin kuruciyarta, Wang Lili ta taba samun matsala da mahaifinta a dalilin buga wasan kwallon kwando, amma ta ce a rayuwarta ta yau da kullum, ita ba mai yawan magana ba ce, idan aka ambato wasan kwallon kwando, sai dai halinta ya canja sosai.

Tun daga lokacin da take buga wasan kwallon kwando tare da yara maza a garinta, wannan mace ta kasance mai muhimmanci a filin wasa, ta kan yi gudu sosai, da yin tsalle sosai, kana ba ta jin tsoron buga wasa a fili. Wang Lili ta ce, wannan ne halinta a filin wasan kwallon kwando.

Wang Lili ta kara da cewa, wani mai horaswa nata ya taba gaya mata cewa, ya kamata a nemi samun nasara a kan wasa, sai dai wasu lokuta a kan cimma nasara ko a ci tura. A ganin Wang Lili, a matsayin wata ’yar wasa, ya kamata a yi hamayya da sauran ’yan wasa, da yin kokarin cimma nasara.

A wannan karo, a yayin tinkarar raunin da ta ji, Wang Lili tana kokarin cimma nasarar daidaita shi. Wang Lili ta kara yin kuzari wajen samun sauki da neman komawa filin wasa cikin sauri. Koda yake akwai sauran watanni 10 kawai suka rage kafin gasar wasannin Olympics ta Paris, amma a sakamakon kokarin da take yi, tawagarta ta yi bincike da cewa, akwai yiwuwar dawowarta filin wasa cikin lokaci. A yayin da ta samu irin wannan rauni lokacin shekaru 24 da haihuwa, ta kashe watanni shida da samun sauki da komawa filin wasa. Amma yayin da shekarunta suka kai 31 da haihuwa a halin yanzu, ya kamata ta kara yin kokari, amma ba ta saduda ba.

A yammacin ranar farkon watan Yunin, kafin ta sake koma filin wasa bayan tiyatar da aka yi mata, Wang Lili ta ambato mafarkin da ta yi ga abokan wasanta, kana ta gaya musu cewa, domin ba ta shiga filin wasa da buga wasa tare da sauran ’yan wasa har na tsawon watanni 8 ba, idan ta gamu da matsala ko ba ta buga wasan da kyau ba, ya kamata su gaya mata a filin.

Lokacin da ta buga wasa a filin wasa, Wang Lili tana ganin ta iya buga wasan kamar lokacin da. Ta bayyana cewa, koda yake tana damuwa kafin buga wasan, amma idan ta shiga filin wasan, babu komai a cikin kwakwalwarta sai wasa kawai, tana cike da hankali kan buga wasan.

wang lili
•Wang Lili suna tare da abokan wasanta a filin wasa

Wang Lili ta ce, idan tana buga wasa a fili, ta kan ji muryoyin abokan wasanta suna cewa, suna bayanta babu damuwa, ta ce, wannan ya karfafa ta, abokan wasanta suna tare da ita.

Ya zuwa yanzu, kungiyar wasan kwallon kwando na mata mai mutane 3 ta kasar Sin ta riga ta samu izinin halartar gasar wasannin Olympics ta Paris da za a gudanar a shekarar bana, za a gabatar da sunayen membobin kungiyar. Wang Lili ta ce, ta taba kai ziyara a birnin Paris lokacin da ta buga gasar wasan a Turai, tana begen samun damar sake zuwa birnin don halartar gasar wasannin Olympics a birnin. (Zainab Zhang)


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: JapanKamfanonin kasar AmurkaSin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Za A Yaki Ciwon Sikila A Nijeriya Daga Tushe – Hajiya Badiyya

Next Post

Aisha Humaira Ta Mayar Da Martani Kan Sace Mahaifiyar Rarara

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

2 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

10 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

11 months ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Salon Dimokuradiyya Mai Sigar Musamman Ta Kasar Sin 
Daga Kasar Sin

Salon Dimokuradiyya Mai Sigar Musamman Ta Kasar Sin 

1 year ago
Next Post
aisha humaira

Aisha Humaira Ta Mayar Da Martani Kan Sace Mahaifiyar Rarara

LABARAI MASU NASABA

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

May 13, 2025
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

May 13, 2025
Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

May 13, 2025
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

May 13, 2025
Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

May 13, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

May 13, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

May 13, 2025
An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

May 13, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.