Rundunar ‘yansandan Jihar Gombe ta kama wani mai unguwa mai shekaru 55 a garin Zambuk da ke Karamar hukumar Yamaltu Deba bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya bayyana wanda ake zargin Mohammed Tukur da ke Kauyen Sabon Gari da ke Zambuk.
- Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama
- Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12
A cewar rundunar ‘yansandan, lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Agusta, da misalin karfe 9 na dare, inda ake zargin wanda ake zargin ya yaudari yarinyar da (aka sakaya sunanta) zuwa wani kebantaccen wuri inda ya aikata laifin.
Ya ce, “Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda na ofishin ‘yan sanda na Zambuk sun yi gaggawar zuwa wurin, inda suka kubutar da wadda abin ya faru, suka kai ta babban asibitin Zambuk, domin a duba lafiyarta.
“Jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda ya bayyana cewa bincike na ci gaba, yana sake jaddada kudirin rundunar na tabbatar da adalci ga wadanda suka fuskanci cin zarafin jima’i.”
“Ya yi Allah wadai da wannan aiki kuma ya yi kira ga mazauna yankin su rika ba da rahoton duk wani lamari na cin zarafin jima’i cikin gaggawa domin bai wa ’yansanda damar sa baki da wuri.”
“An kama wanda ake zargin kuma an kai shi kurkuku nan take.”
Ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da yin kira ga mazauna garin da su gaggauta kai rahoton duk wani abin da ya faru na lalata domin samun damar shiga tsakani na ‘yan sanda kan lokaci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp