Wani mutum mai suna Eze Elechi Amadi ya bayyana dalilin da ya sa ya kashe ƙaninsa mai shekara 18, Otu Ifeanyi, a unguwar Kajola da ke Ƙaramar Hukumar Odigbo, Jihar Ondo.
Amadi, wanda ƴan sanda suka cafke tare da wasu mutum 99 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a Akure, babban birnin jihar, a ƙarshen mako, an kama shi ne a lokacin da yake ƙoƙarin jefar da gawar ƙaninsa da ya kashe.
- Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack
- Kofin Duniya: FIFA Ta Fitar Da Yadda Za A Samu Gurbin Zuwa Amurka
Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Adebowale Lawal, ya bayyana cewa: “A ranar 26 ga watan Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 3 na rana, wani mutum mai suna Oluwafemi Oladipupo na titin Paragon, Kajola, ya kai rahoto a ofishin ƴan sanda na Kajola cewa ya lura da wani duro na roba mai launin shuɗi a gaban gidansa, da aka ɗaure bakinsa da igiya baƙa.”
“Bayan an buɗe duro ɗin, sai aka gano gawar wani matashi mai suna Otu Ifeanyi, mai shekara 18, wanda daga baya aka tabbatar shi ne ƙaninsa wanda ake zargi, a ciki. An gano duro ɗin ne a kan babur da wani mutum mai suna Eze Elechi Amadi yake tuƙawa. Yayin da yake ƙoƙarin kai duro ɗin zuwa wani wurin da ba a sani ba domin jefar da shi, sai ya zame daga kan babur ɗin ya fāɗi.”
Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Ondo, Adebowale Lawal, ya bayyana cewa: “An kama wanda ake zargin nan take. A lokacin da ake masa tambayoyi, ya amsa cewa shi ne ya kashe ƙaninsa saboda rikicin kuɗi, inda ya zargi marigayin da tura Naira 20,000 daga asusun bankin Ecobank ɗinsa ba bisa ƙa’ida ba.
“An ajiye gawar a ɗakin ajiye gawarwaki yayin da bincike ke ci gaba. Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala binciken.”
Da yake magana kan sauran masu laifi da aka kama a faɗin ƙananan hukumomi 18 na jihar, kwamishinan ya ce an cafke su ne bisa zargin aikata laifuka da suka haɗa da: kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami, shiga ƙungiyoyin asiri, mallakar miyagun ƙwayoyi ba bisa doka ba, da sata, da sauransu.
Lawal ya nuna cewa an samu nasarar waɗannan kame ne ta hanyar ƙoƙarin jami’an rundunar da kuma haɗin kan jama’ar jihar, waɗanda suka bayar da sahihan bayanai ga rundunar.
A cewarsa: “A cikin makonnin da suka gabata, rundunarmu ta samu nasarori wajen hana aikata laifuka, gano su, da kuma gurfanar da masu laifi a kotu. Waɗannan nasarori sun nuna ba wai kawai jarumtakar jami’anmu ba, har ma da haɗin kai mai daraja daga mutanen Jihar Ondo”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp