• English
  • Business News
Tuesday, September 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Wasu Iyaye Ke Hana ‘Ya’yansu Auren Matan Da Suka Girme Su Da Zawarawa

by Rabi'at Sidi Bala
3 weeks ago
in Taskira
0
Yadda Wasu Iyaye Ke Hana ‘Ya’yansu Auren Matan Da Suka Girme Su Da Zawarawa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin TASKIRA, shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi al’umma. Ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau, zai yi duba ne game da yadda wasu iyaye mata suke hana yaransu maza auren macen da suke so, musamman idan macen ta fi su shekaru ko kuma ta taba aure. Wanda hakan ke ci wa wasu matan tuwo a kwarya, musamman wadanda ke fuskantar irin wannan matsalar, ganin sun samu mijin aure amma uwar mijin ta hana auren.

  • Hadin Tuwon Dawa
  • Sin Ta Bukaci Japan Da Ta Yi Karatun Baya Game Da Batutuwan Tarihi Da Suka Shude Irinsu Batun Wurin Bauta Na Yasukuni

Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiyan sa game da wannan batu; “Me za a ce a kan hakan?, wane amfani ko rashin amfani hakan yake da shi?, Ko akwai wasu matsaloli da hakan zai iya haifarwa?, wacce shawara za a bawa iyaye mata masu aikata hakan?”. Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Abba Abubakar Yakubu daga Jos, Jihar Filato:

A nawa ra’ayin wannan kuskure ne da bai dace a ce iyaye suna shiga hurumin ‘ya’yan su ba, musamman game da zabin matar aure ko mijin aure. E, babu laifi iyaye su bai wa dansu ko ‘yar su shawara kan zabin da, suka yi, a inda suke ganin wanda za su kawo cikin rayuwarsu na da wata illa da ta shafi addininsa ko mutuncin sa da makomar rayuwarsa. Hakan na zama da, muhimmanci ne a inda dan nasu ko ‘yar su ke da karancin shekaru ko wayewa, yadda ake ganin ba za ta iya tantance nagari da mugu ba. Amma idan har bambancin da ake gani bai wuce bambanci na shekaru ko matakin rayuwa ba, ya kamata a kyale ta ko shi su auri wanda zuciyar su tafi kwantawa da shi. Sau da dama an fi samun wannan kalubale a wajen iyaye mata, da ke ganin dansu saurayi ne bai dace ya fara aure da bazawara ba, ko wacce suke gani ta girme masa a shekaru. Tunanin su shi ne dan su ba zai ji dadin aure ba, don matar za ta fi shi wayo, saboda ta fi shi sanin aure, za ta zama ita ce ke sarrafa zamantakewar su, ba shi ba. Su kuma iyaye mata ba sa so a ce ga, wata nan tana yi wa dansu wayo, ko a ce ita ce ke juya shi. Ba a cika samun irin haka a wajen mata ba, wanda dama su an fi so su auri wanda ya girme musu, don ya kula da tarbiyyar ta da rayuwarta, kuma ya rika gyara mata yadda take tafiyar da rayuwa. Sai dai a inda mijin da za ta aura yana da wata matar ko wasu matan da suka girme mata, inda za a fara tunanin za su azabtar da ita, ko za su bata wahala a zaman kishi da za su yi. Gaskiya yana da kyau iyaye su daina hukunci kan makomar ‘ya’yan su da irin wannan tsohon tunani da ba shi da wata fa’ida. A kyale yara su auri wanda suke so, matukar an amince da addininsu da tarbiyyar su, da ingancin lafiyar su, da sauran muhimman abubuwa da ake dubawa wajen samar da aure ingantacce.

Labarai Masu Nasaba

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa

 

Sunana Princess Fatimah Mazadu daga Jihar Gomben Nijeriya:

To, Allah ya kyauta. Amma wannan babban kuskure ne, shi kanshi manzon mu Annabi Muhammadu (SAW) da bazawara ya fara, kuma wacce ta girme masa nesa ba kusa ba. Me yasa ba za a bi sunna ba, kamar yadda ake bin hafisi da fikhu ake karanta abun da Allah yace “Kuran”. Kuskure ne babba, ba kai za ka zauna da matar ba, ka bar mai zama da ita ya auri ra’ayinsa, saboda gujewa rigima da da-na-sani. Babu wani amfani sai tozarci da cin mutuncin kaddara, wanda ita mai hanawar ba ta fi karfin ta dawo bazawarar ba. Mata su kiyaye wannan bakin akidar, saboda gyara nasa da na sauran ‘yan’uwa, in ba ki da ‘ya mace ‘yar’uwarki na da ita, kuma in auren ta ya mutu ya za ku yi da ita. Eh! to, matsaloli kam akwai dan iyaye in suka kafe akan kar ka yi auren ka barshi, dan ko an yi matar za ta shiga uku da kyara da tsangwama. Iyaye su yarda da kaddara da kuma bawa yaransu dama su auri abun da suke so in har bai kaucewa shari’ar musulumci ba, gudun baraka da gigitar lamura.

 

Sunana Muhammad Isah Zareku Miga A Jihar Jigawa:

A gaskiya akwai iyayen da basa son dansu ya auri wacce ta girmi dansu ko kuma bazawara, kuma yin hakan ba daidai bane. Auren babbar mace ko bazawara ai ba shi da wani aibu ko matsala yana da amfani, sannan kuma idan ba a aurensu to, su waye za su aure su. Ni a ganina ya dace a auri bazawara ko babbar mace, hakan ba laifi bane. Shawarar da zan bawa iyaye mata a nan shi ne; aure akan macen da ta girme su ko kuma bazawara indai ba wata matsala ce da ita ba su barshi ya aure ta, saboda Manzon Allah (S.A.W) ai ya auri bazawara wato Nana Khadija.

 

Sunana Hafsat Sa’eed daga Jihar Neja:

A nawa ganin hakan ba tsarin musulunci ba ne, ko Annabi (s.a.w) da bazawara ya fara, kuma ta girme shi ma a shekaru. Ni ina ganin ba wani amfani ko rashin amfani, ra’ayi ne na dan’adam kowa da ra’ayinsa da kuma irin abin da yake so. Babu wani matsaloli da yake haifarwa, indai akwai so akwai kauna, akwai zaman lafiya, babu wani matsala da zai haifar yin hakan illah iyaka zaman lafiya. Shawarar da zan bawa iyaye shi ne, su bar yaransu su rika auren wadanda suke so, saboda muddin tana da tarbiyya, tana da halin mai kyau, ta fito daga gidan mutumci, idan yaro ya kawo yana so ya kamata a barshi ya aure ta. Saboda rashin auren abin da ka ke so, shi yake jefa mutane a duk irin wannan matsaloli da abubuwan da ake tsintar kai a ciki.

 

Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:

Wannan dabi’a ba ta dace ba, domin ta takaita ‘yancin yaro wajen zabar abokiyar rayuwa bisa soyayya da fahimta. Iyaye na iya ba da shawara, amma hana aure gabadaya saboda shekaru ko matsayin mace (bazawara) abu ne da zai iya tauye rayuwar da. Fa’ida: wasu iyaye na ganin cewa ‘yar aramar yarinya za ta fi saukin sarrafawa, ko kuma za ta fi dacewa da yaron a dogon lokaci. Rashin fa’ida: Yana iya haddasa rashin zaman lafiya a rayuwar aure idan yaron ba ya son matar da aka zaba masa. Haka kuma, yana iya jefa mace cikin damuwa da ciwon zuciya idan aka hana ta mijin da take so. Yaro na iya yin aure ba tare da jin dadin zuciyarsa ba. Zai iya guje wa aure gabadaya, zai iya rasa damar samun mace mai kima saboda matsin iyaye, zai iya jefa soyayya a cikin barnar da ba za a iya gyarawa ba. Shawara ga iyaye, su saurari ra’ayin ‘ya’yansu cikin hikima da adalci. Su duba tarbiyya, halayya da kamun kai fiye da shekaru ko matsayin mace. Su taimaka wajen tabbatar da farinciki da zaman lafiya a rayuwar aure, ba wai su hana hakan ba.

 

Sunana Maryam Muhammad Kabeer, daga Jihar Kano:

Wannan wata matsala ce wacce take damun wasu daga cikin ‘yan’uwa mata, dan wata na son ta yi aure amma sai ki ga iyayen saurayin ko mahaifiyarsa ta kafe lallai ba zai aure ta ba, ta yi masa girma ko kuma ta taba auren wani namijin, to, ba shi ya gani ya ce yana so ba. Wannan abun iyaye mata ne suka fi yanke hukumcinsa. Ni ina mamaki wallahi kamar ba mace ce ‘yar’uwarta ba, ita ba ta tunanin kaddara ta biyo ta kanta ko kan ‘yarta, Allah dai ya kyauta. Kawai indai mace ba ta da wani aibu daga cikin abun da ake buncike barshi ya auri abarsa. Hakan a gaskiya bashi da wani alfanu, dan gara a bar yaro ya auri wadda ran shi yake so saboda da shi zasu zauna, ba da iyayen ba, kuma shi aure ba a duban shekarun mutum, abin da suke da muhimmanci a duba sune kamar, iliminta(addininta), nasabarta da dai sauransu.

 

Sunana Anas Bn Malik Achilafiya, Karamar Hukumar Ƴankwashi, Jihar Jigawa:

A gani na irin wannan ba ya rasa nasaba da yadda ake samu yawanci matan da suka girmi namiji suna da wasu ‘ya’yan daban, shi ya sa sai iyaye su hana yin auren ko nuna kyama. Amma idan har ba ta taba haihuwa ba, ana samun amincewa ba kamar wadda ta ke da ‘ya’ya ba, sai dai ko idan tana da wasu halaye marasa kyau da za su sanya a guje ta. Auren macen da ta girme ka, matukar tana da kyawawan halaye, namijin yana ribatar abubuwa da yawa kamar haka; Kulawa fiye da ta wanda shi mijin ya girme ta, dan ita a lokacin ta fi bukatar kulawarka, sabanin ita yanzu ta fi ka shekaru, dan haka watakila ta fi ka sanin rayuwa. Mutuntawa fiye da ta wadda ka girme ta, ita zaman jiran haka ta ke, ita kuwa yanzu tana jin kai ke bukatar haka fiye da ita, dan ka riga ka yi mata komai, tunda har ka aminta da ita, duk da irin tazarar shekarunta da na ka. Da dai sauransu. Tabbas ba za a rasa matsaloli ba, amma dai matsalolin ba za su yi tasirin kawo karshen auren ba, matukar an samu fahimtar juna tun kafin yin auren. A karshe shawara ba ta wuce iyaye su bar namiji ya auri wacce suka fahimci juna, koda kuwa ta fi shi shekaru, matukar dai tana da kyawawan halaye da za ta tarbiyyantar da iyalansa, tare da mu’amalantar ‘yan’uwa da abokan arzuka. Allah ya sa mu dace, ya sa mu cika da imani.

 

Sunana Hafiza Abbas daga Katsina:

Wannan abun da iyaye ke yi wani salo ne da mafi yawansu ke yi ga ‘ya’yayensu da mabambantan manufa, wadansu dan hangen nesa da hango abin da ka iya faruwa bayan aure, wadansu kuma wata manufar ta kiyayyar da ke zuciyarsu kan wacce ya nemo. Amfani a nan kuwa shi ne, abun da babba ya hango yaro ba zai hango ba, domin su iyaye sun fi mu dadewa a duniyar, sun ga a bin da ba mu taba haduwa da shi ba, wasu iyayen sun ga matsalolin da hakan ya haifar sakamakon yin aure a haka. Tabbas a nawa ganin akwai matsaloli da hakan ka iya haifarwa, kamar idan aka yi aure a haka wasu matan suna kudurta juya gidan da yi wa maigidan wayo, wanda hakan ba abu ne da ya kamata ba. Shawarata ita ce iyaye su dubi manufar yanke hukumcin da suka yi, mai kyau ce ko kuwa?, su ji kuma ta bakin ‘ya’yayen abun da ke ransu, su shawarci yaran tare da kawo misalai kala-kala wadanda za su gamsar da yaran.

 

Sunana Ibrahim Garba Bizi Damaturu, Jihar Yobe:

Wannan hali yana nuna tsangwama ko rashin adalci a cikin zabi na aure, aure ya kamata ya zama zabin mutum da yardarsa, ba dole daga iyaye ba, musamman idan babu laifi ko wata matsala ga wacce zai aura. Amfani (ra’ayin wasu iyaye): suna ganin yarinya karama za ta fi saukin gyarawa, zai fi saukin mulki da jituwa da dangin miji. Zai iya haifar da aure mara jin dadi, zai iya saka dan ya gudu ko ya boye aure, zai jawo rikici a cikin iyali da auratayya mara kkwanciyar hankali. Ku ji ra’ayin danku, kuma ku ba shi dama ya zabi wacce yake so. Ku gane cewa bazawara ko wacce ta girma da da ba laifi ba ne.

 

Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:

Lallai akwai iyaye masu irin wannan hali na hana ‘ya’yansu abin da ransu yake so koda ko hakan bai saba da addini ko al’ada ba, kuma hakan bai dace ba, donim kowa da abin da ransa yake so. Rashin amfanin hakan shi ne tauye hakkin yaro da kuma rashin cika burinsa na rayuwa domin auren babbar mace indai ta kirkice to babu shakka abu ne mai kyau. Hakan zai iya haifar da abubuwa masu yawa daga ciki akwai cirewa yaro son auren gabadaya, sannan hakan na iya sa su rika kebanta da juna suna badala, kuma hakan zai iya zama sanadin sabawarsa da iyayensa. Shawara a nan ita ce indai iyaye sun yarda da tarbiyyar mace da kuma addininta to kada su hana dansu aurenta in ya ce ita yake so, don gudun abin da zai iya faruwa sakamakon hanawar.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:

Hakan yana faruwa sosai, kuma ba abu ne mai kyau ba. Iyaye kawai mu nema wa ‘ya’yanmu mataye nagari masu addini shi ne, kai ma fa hakan zai iya faruwa akan naka dan ato, idan ba a auren masu shekaru da zawarawan ina za a kai su dan Allah?. Matsala ce babba dan za ta jawo yaranmu su lalace suna son auren wani rashin dalili ya hana. Iyaye su yi hakuri kawai indai abu bai shafi addini ba, su rika ragewa suna bawa yaransu dama.

 

Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano LGA, Jihar Kano:

Hana namiji ya auri bazawara ko macen da ta fi shi shekaru bai dace ba, indai har ita wannan matar ba wai iyayen yaron sun hango akwai wata cutarwa da za ta biyo baya ba. Domin manzon tsira ma matarsa ta farko bazawara ce, kuma ta fi shi shekaru, kin ga kuwa barin yaro ya aura ma ya aikata wata babbar sunnah ce. Amfanin hakan an dabbaka wata babbar sunnah ne a cikin sunnar Annabi. Indai da so da kaunar juna ni dai sai na ga babu wata matsala, sabida mafiya irin wannan auren ma ya fi dankon soyayya da girmama juna. Saboda ita macen za ta rika girmama shi a matsayin miji, haka shi ma zai rika bata wani girma na ganin ta fi shi shekaru. Shawarata a nan indai ba sun tabbatar akwai wata cutarwa a wannan auren ba to, gaskiya kada su hana tunda aure ne ba wai wani zama na haka kawai ba, kamar yadda na fada wanda ya zo mana da addinin ma ya auri bazawara kuma wadda ta fi shi shekaru. Allah ya sa mu dace, amin.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Auren
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hadin Tuwon Dawa

Next Post

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

Related

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?
Taskira

Me Ya Sa Wasu Maza Ke Gudun Auren Mata ‘Yan Boko Masu Kwarewa Da Wayewa?

1 week ago
Auren
Taskira

Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa

1 month ago
Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri
Taskira

Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

2 months ago
‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
Taskira

Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah

5 months ago
Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan
Taskira

Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan

6 months ago
Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?
Taskira

Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?

7 months ago
Next Post
Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

Na Hadu Da Azzalumai Da Mayaudara Farkon Shigata Kannywood – Dan’duniya

LABARAI MASU NASABA

Neman Gurbi: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Afirka Ta Kudu A Bloemfontein

Neman Gurbi: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Afirka Ta Kudu A Bloemfontein

September 9, 2025
Nan Gaba TIinubu A Wajen Opay Da Moniepoint Zai Nemi Rancen Kuɗi – Dino Melaye

Nan Gaba TIinubu A Wajen Opay Da Moniepoint Zai Nemi Rancen Kuɗi – Dino Melaye

September 9, 2025
Kotu Ta Umarci A Kamo Mata Dogarin Gwamna El-Rufa’i

El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙara Kan Zargin Ƴansanda Da Cin Zarafinsa A Kaduna

September 9, 2025
Gwamnatin Jigawa Ta Dage Komawa Makaranta Saboda Kidayar Jama’a

Gini Ya Rushe A Jigawa, Mutum 1 Ya Rasu, 7 Sun Jikkata

September 9, 2025
Kasar Sin Ta Zama Wurin Da Aka Fi Zaba Domin Warware Takaddamar Cinikayya Da Ta Shafi Kasa Da Kasa

Kasar Sin Ta Zama Wurin Da Aka Fi Zaba Domin Warware Takaddamar Cinikayya Da Ta Shafi Kasa Da Kasa

September 8, 2025
Sojoji

Sojoji Sun Kai Hare-hare 261, ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 1,950 A Watan Agusta – NOA

September 8, 2025
Kasar Sin Ta Bayar Da Gaggarumar Gudunmuwa Ga Wanzuwar Zaman Lafiya Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Ta Bayar Da Gaggarumar Gudunmuwa Ga Wanzuwar Zaman Lafiya Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 8, 2025
'yansanda

An Kama Mutane 30 Da Zargin Laifin Aikin Dabanci A Yayin Zagayen Maulidi A Neja

September 8, 2025
Xi Jinping Ya Aika Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Cifit Karo Na 25

Xi Jinping Ya Aika Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Cifit Karo Na 25

September 8, 2025
Gwamnatin Tarayya, NUPENG Da ÆŠangote Sun Fara Tattaunawa Don Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Ma’aikatan Mai

Gwamnatin Tarayya, NUPENG Da ÆŠangote Sun Fara Tattaunawa Don Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Ma’aikatan Mai

September 8, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.