Fafatawar yaki a tsakanin kasashen Iran da Isra’ila na ci-gaba da daukar hankalin al’ummar duniya bakidaya tare da sanya fargaba da zullumin yadda yakin zai zama kuma ya kasance.
Masana na ganin yakin zai iya zama hadari da koma baya ga kasashe da dama ciki har da Nijeriya a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke ci-gaba da tabarbarewa.
- Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?
- Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump
Yakin da ake ci-gaba da gwabzawa tsakanin kasashen wanda ya girgiza duniya bakidaya zai iya shafar tattalin arzikin Nijeriya ta fuskoki da dama.
Tun da farko dai Nijeriya kamar sauran kasashen Afurka tuni ta yi tir da matakin da Isra’ila ta dauka na kaiwa Iran hari ta na cewar hakan zai haifar da gagarumar matsalar da ba a san karshen illar ta ba.
Gumurzun Iran da Isra’ila da aka fara a ranar 13 ga Yuni 2025, ya riga ya yi tasiri ga tattalin arzikin duniya wanda ya haifar da rashin tabbas, karin kudin albarkatun mai da cikas ga kasuwanci da fitar da kaya a kasashe.
Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin farashin abubuwa da dama da zai hau sama.
A cewar masana, Gabas ta Tsakiya da ke samar da akalla kashi 34 na mai a duniya da kashi 18 na gas, gumurzun kasashen biyu ya haddasa farashin danyen mai tashi da kashi 10, yayin da gas ya kara da kashi 7. Haka ma akwai fargabar Isra’ila na iya illata harkokin mai da jigilarsa a mashigar Hormuz da ke karkashin ikon Iran.
Baya ga wannan farashin rarraba kaya da fitar da kaya ta jiragen ruwa ya karu a bisa ga tashin kudin inshoran jiragen ruwa a Gabas ta Tsakiya wanda ya kawo tsaikon kasuwanci a duniya.
A yanzu haka dai a wannan makon kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya fitar da sanarwar karin kudin mai a gidajen man sa a fadin kasar bakidaya.
Tun a kwanan baya masana suka bayyana cewar farashin man fetur zai tashi a kasuwannin duniya a dalilin fafatawar yakin Iran da Isra’ila.
Kamfanin ya bayyana karin kudin mai zuwa naira 945 wanda karin ya biyo bayan karin kudin mai da matatar mai ta Dangote mai zaman kan ta ta yi zuwa naira 880.
A bayyana yake cewar Iran babbar kasa ce daga cikin manyan kasashen duniya masu karfin arzikin man fetur da ke fitar da shi a kasashen duniya don haka wajibi ne yaki da kasar ya shafi tattalin arzikin kasashe da dama.
Duk da matatar mai ta Dangote ta na aiki amma har zuwa yanzu shigo da man fetur ake yi a Nijeriya don haka tashin farashin a kasuwannin duniya na nufin tashin farashinsa a Nijeriya kamar yadda masana suka bayyana.
Da yake bayani kan illar yakin ga Nijeriya, masani kan tattalin arziki da huldar diflomasiyya kuma Shehin Malami a jami’ar Ibadan, Farfesa Tayo Bello ya yi gargadin yakin zai shafi Nijeriya da babban kalubale sosai.
Ya ce Nijeriya wadda ita ce babbar kasar Afurka mafi albarkatun mai za ta ci-gaba da amfana da karin kudin mai a gajeren lokaci, amma hakan zai haifar da gagarumar illa ga ‘yan Nijeriya a gida.
“Yakin tamkar takobi biyu ne mai kaifi ga Nijeriya, a daya hannu a na tsammanin farashin mai a kasuwar duniya zai tashi sosai. Hakan na nufin Nijeriya za ta ci-gaba da samun karin haraji sosai musamman idan farashin ya tashi daga dala 75 a ganga daya zuwa dala 90 ko sama da haka.”
“Karin kudin mai a duniya na nufin karin kudin mai a Nijeriya. Man dizel, fetur da sauran abubuwa za su yi tsada sosai wanda hakan na nufin hauhawar farashi sosai.”
Injiniya Yabagi Sani fitaccen mai sharhi kan al’ummarran man fetur a Nijeriya ya bayyanawa BBC Hausa cewar illar da yakin ya yi wa sauran kasashen duniya shine ya shafi Nijeriya.
Ya ce a bayyane yake kusan kashi 20 zuwa 30 na mai da ake hada- hadarsa a kasuwannin duniya a na yin sa ne ta mashigar Hormuz da ke karkashin kasar Iran don haka su ke da ikon shiga da ficen mai.
Masanin ya bayyana cewar a sakamakon wannan yakin Iran ta yi barazanar rufe mashigar wanda sakamakon fargabar matsalar da za ta iya biyowa baya, jiragen dakon man fetur suka fara kauracewa mashigar wanda a cewarsa wannan ne ya haifar da karancin mai a kasuwandnin duniya bakidaya.”
Shi kuwa tsohon jakadan Nijeriya a kasar Ethiopia, Bulus Lolo na ganin ko kadan ba alheri ba ne ga kowa ciki har da Nijeriya kan ci-gaba da nunawa juna yatsa da kasashen biyu ke yi.
Ya ce a wasu lokutan fada irin wannan yana da amfani, a wasu lokutan kuma ba ya da amfani. Nijeriya ba ta fuskantar farmaki kai tsaye, amma ta na amayar da muryar ta kan kasashen biyu da su tsagaita wuta su daina kaiwa juna hari, a zauna a teburin sulhu.*
Ya ce kasuwar mai a duniya za ta shaidi artabun da ke faruwa a ma’ajiyar man Iran, amma ba su fatar kazantar lamariin a kasuwar duniya, a cewarsa suna fatar abubuwa za su daidaita domin hasashen su ya tafi daidai.
“Akwai yiyuwar karin kudi ta yadda farashi zai hau sama sosai amma har zuwa yaushe? Sabani ne wanda ba mu san yadda karshensa zai kasance ba.” In ji Lolo.
Masana da jama’a na ganin mafitar kawar da radadin farashin mai a Nijeriya shine gwamnafi ta inganta matatun mai, ta yadda za su rika aiki yadda ya kamata domin samar da wadataccen mai ga ‘yan kasa.
Haka ma gwamnati za ta iya saukakawa jama’a ta hanyar rage farashin mai wanda hakan zai magance hauhawar farashin kaya da al’umma ke fargaba a halin yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp