Shugaban Kungiyar Manoman Alkama, reshen Jihar Gombe; Lawan Bala Garba, ya bayyana damuwarsa kan yadda yakin da ake ci gaba da gwabzawa a Kasashen Ukraine da Sudan; ke shafar noman Alkama a fadin duniya.
Ya sanar da cewa, yakin ya kuma haifar da karancin samun Iri na Alkama, musamman a Jihar Gombe, wanda hakan ya hana manoma samun damar shuka Irin Alkama, domin noman rani.
- Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 181, Sun Cafke 203 A Cikin Mako Guda – Hedikwatar Tsaro
Lawan ya ci gaba da cewa, kasar ta Ukraine ita ce kan gaba a duniya wajen noman Alkamar, amma yakin da ake yi a kasar ya shafi nomanta a Jihar Gombe.
Kazalika, ya sanar da cewa; Kasar Sudan wacce ita ma tana kan gaba wajen noman Alkamar a Nahiyar Afirka, yakin da ake yi a kasar ya sanya gaza yin nomanta yadda ya kamata.
A cewarsa, yake-yaken wadannan kasashe biyu, ya haifar da karancin samun Irin Alkamar a duniya, ciki har da Nijeriya.
Shugaban ya ci gaba da cewa, rashin samun wadataccen Iri na Alkama a kasuwanni, ya haifar da rashin yin noman ranin a bana, duba da kakar noman ranin na bana, na kara karatowa.
A cewarsa, idan manoman ba su samu Irin Alkamar a karshen watan Dismabar 2024 ba, za su yi babbar asara; ko da kuwa daga baya an samu wadataccen Irin Alkamar.
Lawan ya ci gaba da cewa, hauhawar farashin fulawa; ya kara jawo munanar al’amarin, duba da yadda ake sarrafa Alkamar zuwa fulawa, ba tare da an adana Irin shukarta ba.
A cewarsa, a kasuwannin Jihar Gombe, ba a samu wadatacciyar Alkamar ba, ballatana maganar samun ingantaccen Irinta da za shuka.
Ya yi nuni da cewa, bukatar da ake da ita ta Alkamar ya karu, kuma sauran Irin noman nata da suka yi saura, tuni duk an cinye su.
Sannan, ya bukaci gwamnati ta kawo dauki; musamman wajen samar da wadataccen Irin nomanta.
Shugaban ya kuma bayyana cewa, noman Alkama a Jihar Gombe; na kara zama fitacce, sakamakon yadda ake samun dimbin kudaden shiga daga fannin.
Lawan ya ci gaba da cewa, sama da manoman Alkamar 9,000 a jihar yanzu; suna noma Alkama a duk shekara; inda Karamar Hukumar Nafada, ta kasance a kan gaba.
A cewar tasa, yanzu a Karamar Hukumar ta Nafada, ana iya yin tunkahon cewa, akwai kadadar noman Alkamar sama da 3,000.
Shugaban ya kuma bukaci manoman jihar, su rungumi dabarun adana Irin Alkamar, mai makon sayar da shi; bayan kammala girbi.
A cewarsa, dole ne manoman su rika gujewa sayar da Irin da suke da shi gaba daya duk da cewa, ana samun makudan kudade idan aka sayar da Irin.
Shugaban ya kara da cewa, gazawar adana Irin; zai jawo musu gagarumar matsala a kakar noma ta gaba.
Lawan ya kuma jaddada muhimmancin gwamnati, wajen kawo daukin gaggawa; domin ganin yadda noman Alkamar ke kara lalacewa a yankin.