Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da fasinjoji 20 a kan hanyar da ta hada Mariga da Karamar Hukumar Kontagora a Jihar Neja.
Fasinjojin na tafiya ne a kan titin, yayin da ‘yan fashin, suka sauke su daga mota suka tilasta musu shiga wani dajin da ke kusa.
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Singapore Da Azerbaijan
- An Kama Wasu Ƴansanda Kan Zargin Kisan Ɗalibin Jami’ar Kwara
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkin-Daji, mai wakiltar mazabar Mariga, ya tabbatar da sace mutanen a ranar Alhamis. Kalaman nasa sun biyo bayan kin amincewar da sojoji suka yi na kai hare-haren ‘yan bindiga a wuraren horar da sojoji da suka hada da Kananan Hukumomin Kontagora da Mariga.
Ya shaida wa manema labarai lamarin ya faru ne a yayin da ‘yan bindiga suka tare hanyar Mariga zuwa Kontagora tsakanin Baban-Lamba da Beri.
Shugaban majalisar ya kara da cewa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a baya sun rika karbar kudaden fansa a wani yanki dazuzzuka, wanda aka ruwaito a kusa da filin horar da sojoji. Wadanda abin ya shafa sun shaida wa iyalansu cewa an tsare su ne a kusa da Barikin Sojoji na Kontagora.
Sarkin-Daji ya bukaci sojoji da su yi aiki da sahihan bayanai tare da kawar da ‘yan fashin daga yankin, yana mai cewa, “Fasinjojin da aka yi garkuwa da su a ranar Alhamis a hanyar Mariga zuwa Kontagora, an kai su dajin guda.”
Shugaban majalisar ya jaddada cewa, a matsayinsu na wakilan jama’a, ‘yan majalisar su kan sami amsa kai tsaye daga ‘yan mazabar kan wahalhalun da suke ciki, kuma suna yin nazari sosai kan wadannan batutuwa kafin su gabatar da su gaban majalisar.
Yayin da yake amincewa da karfin soja na yaki da ‘yan fashi, ya yi gargadi game da watsi da korafe-korafen mazabar.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya shafa da su shawo kan wadannan matsalolin, inda ya bayyana cewa al’ummomin yankin na zargin wuraren horar da sojoji sun zama mafakar ‘yan bindiga.
“Hatta wadanda aka sako bayan an biya kudin fansa sun bayyana cewa an tsare su ne a gaban Barikin Sojojin Kontagora,” a cewar Sarkin-Daji.
“Sojoji su tabbatar da bayanan wadanda abin ya shafa kan su magance matsalar, maimakon yin watsi da maganganun da ‘yan majalisar suka yi.”
Duk da korar da sojoji suka yi a baya na furucin dan Majalisar daya, ‘yan bindiga sun tare hanyar Baban-Lamba zuwa Beri inda suka yi awon gaba da fasinjoji sama da 20 tare da mayar da su daji guda.
Shugaban majalisar ya yi kira ga sojoji da su kori miyagu daga yankin tare da jaddada cewa majalisar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a don tabbatar da gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki sun fahimci halin da jama’a ke ciki.