Yayin da Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya bayar da hutun kwana 2 ga ma’aikatan jihar don samun damar yin rajistar katin zabe na dindindin (PVCs), wakilinmu da ya za gaya rumfunan katin zaben ya ce, mutane sun bijirewa mamakon ruwan sama da rana domin yin rajistar.
Ya bayyana cewa, jama’ar jihar sun hallara a rumfunan da adadinsu mai yawa.
A ofishin hukumar zabe ta kasa INEC dake kan titin Miango a karamar hukumar Jos ta kudu, jama’a sun sha mamakon ruwa akansu, sannan sun tsaya cikin haquri a kan layi domin a yi musu rajistar.
Har ila yau, a karamar hukumar Jos ta Arewa an ga dimbin jama’a sun yi tururuwa a cibiyar da nufin suma ayi musu rajistar.
Daya daga cikin wadanda ke cibiyar, Charity Sani ta koka kan karancin kayan aiki da ma’aikatan na INEC, inda ta bayyana cewa rajistar na tafiya a hankali.
Ta roki INEC da ta tura isassun ma’aikata da kayan aiki domin samun damar yin rijistar adadin mutanen da ya kamata.
Da yake zantawa da LEADERSHIP, shugaban wayar da kai da ilimantar da masu kada kuri’a na hukumar zabe ta kasa INEC reshen jihar Filato, M. Egurube Michael Otukpa ya ce jama’a sun musu yawa ne.