Akwai amosanin ciki, wanda kan rikide daga karshe yake komawa warin baki ga mace ko namiji.
Hakan ba karamar baradana ya kan haifar wurin duk wanda yake dauke da wannan larurarba.
- Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
- ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu
Don kuwa ya kan sanya a rika kyarar mutum ko kuma yi masa kallon wanda ba ya kula da tsaftar bakinsa, wanda a zahirin gaskiya ba hakan bane ciwo ne wanda babu yadda mutum ya iya.
Don haka duk wanda yake fama da irin wannan larurar ta amosanin ciki ko na baki sai ya nemi maganin amosanin baki
Abubuwan Bukata:
Kanunfari kamar guda bakwai 7, daidai lokacin da za a kwanta barci a rika taunawa ana hadiye ruwan.
Ko kuma a nemi man kanumfarin a rika shan karamin cokali kafin kwanciya barci.
In sha Allah za a rabu da wannan matsalar.
A samu zuma tatacciya mai kyau mara hadi a dinga wanke baki da ita safe da yamma tsawon sati 2 in sha Allah za’a rabu da warin baki.
Allah ta’ala ya sa mudace
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp