A ‘Yan kwanakin nan, kwamitin ladabtarwa na Gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) ta hukunta kungiyar kwallon kafa ta Katsina United bayan abinda ta kira rashin samar da jami’an tsaro a wasan da ta karbi bakuncin takwararta ta Barau Fc a wasan Mako na 12 na Gasar Firimiyar Nijeriya da suka buga a filin wasa na Muhammad Dikko dake birnin Katsina.
Kafin hukuncin na Katsina, kwamitin ya kuma hukunta kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars kwatankwacin hukuncin da ta yi wa Katsina United da ya hada da biyan tarar Naira miliyan 9 da kuma dakatar da wasanni a filin wasanta na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano, hakan ya janyo cece-kuce a tsakanin masu sha’awar kallon wasan kwallon kafa musamman. a jihohin da abin ya shafa na Katsina da Kano.
A yau Leadership Hausa ta zakulo maku wasu hanyoyin da ka iya takaita yawaitar fadace-fadace yayin buga wasannin Firimiyar Nijeriya
Amfani da jami’an tsaro:
Abu na farko dai dole ne kungiyoyi su yi aiki tare da yansanda, NSCDC, da jami’an tsaro na sirri wajen tsara tsare-tsaren tsaro a ranar da za su buga wasa, domin kuwa Bahaushe na cewa, “tun za a, ake shiri ba sai an dawo ba”, hakazalika yana da mahimmanci a tura isassun masu aikin kwantar da tarzoma (ba yansanda kawai ba) don sa ido kan magoya baya, lura da wuraren shiga/fita, da kuma taimakawa wajen rage turmutsitsi yayin wasa.
Amfani da CCTV:
Yawancin filayen wasa na gasar NPFL ba su da isasshen tsarin kyamarar CCTV, a cikin filayensu cewar bincike, samar da kyamarori masu sa ido na iya rage tashin hankali a cikin filayen wasa domin idan an ga wani motsi da ba a yarda dashi ba sai akai dauki da wuri.
Shingaye:
A tabbatar da cewa akwai shingen tsaro tsakanin yan kallo da cikin filin wanda ke hana saurin shiga filin wasa, bincike ya nuna wasu filayen gasar NPFL ba su da wani shamaki tsakanin yan kallo da filin wasa, hakazalika akwai bukatar raba magoya bayan kungiyoyin dake buga wasa zuwa mabanbantan wuraren zama, wannan yana rage rikici kai tsaye.
Matakan Ladabtarwa Masu Tsauri:
Hukumar NPFL ta riga ta sanya takunkumi mai tsanani ga Kano Pillars bayan wani tashin hankali da aka yi a wasanta da 3SC inda akaci kungiyar tarar Naira miliyan 9 da rabi, rage maki da kwallaye, da kuma rufe filin wasansu na gida a yanzu.
Hukunta Laifuka:
Ya kamata a gano wadanda suka mamaye filin wasa ko suka kai hari ga yan wasa da jami’ai (ta hanyar CCTV) kuma a gurfanar da su a gaban kuliya, wannan zai rage rikici a cikin filayen wasa.
Wayar Da Kai:
Akwai bukatar ci gaba da ilmantar da magoya baya kan halaye masu kyau, hatsarin tashin hankali, da kuma girmama jami’an wasa, kungiyoyi da NPFL za su iya gudanar da bita na magoya baya, amfani da kafofin sada zumunta, da kuma amfani da kungiyoyin magoya baya.
Rahoton Wasanni:
Bayan kowace wasa da aka buga akwai bukatar a gabatar da cikakken rahoto akan yadda wasan ya gudana, ta hakanan Za’a iya gano wuraren da suke bukatar gyara domin gyarawa kafin buga wasan gaba, hakazalika za a iya gano wanda ya nuna halayen rashin da’a a wasan domin a hukunta shi.
Jawo Hankalin Matasa:
Yawancin abubuwan tashin hankali suna faruwa ne da saka hannun matasa, saboda a cikinsu ne ake samun magoya baya masu zuciya da saurin fusata, akwai bukatar a nuna masu wasan kwallo WASANE BA FADA BA, mahukunta su shiga makarantu, majalisun matasa, da shugabannin al’umma domin sanar dasu ilimin kwallon kafa don koyar da girmamawa, wasa mai kyau, da kuma nusar dasu illolin tashin hankali.
Inganta Tsarin Shiga Filin Wasa:
Ayi amfani da hanyoyin zamani musamman na dijital wajen bayar da tikitin shiga filayen wasa da kuma guje wa cunkoso, idan da hali ana iya saka bayanan duk wanda ya shiga filin wasa wanda zai sa idan wani ya aikata laifi zai yi saukin kamawa ga hukuma.
Sakon Neman Afuwa Ga Jama’a Da Jagoranci:
Shugabannin kungiyoyi (kamar Ahmed Musa na Pillars) ya kamata su ci gaba da yin kira ga jama’a game da illar tashin hankali, amma kuma suyi hakan ta hanyar da magoya baya zasu gamsu kuma su fahimci abinda ake bukatar su Sani, Musa ya riga ya nemi afuwa a bainar jama’a kuma ya yi alkawarin daukar mataki.













