Shugaban kungiyar Fulani makiyya ta kasa reshen jihar Bauchi Miyetti Allah ta bayyana cewa, dawo da amfani da burtaloli kasar nan ne kawai mafita kan kawo karshen ricikin da ke ci gaba da aukuwa a tsakanin manoma da makiyyan kasar nan.
Shugaban kungiyar reshen jihar Alhaji Sadikue Ibrahim Ahmed a wata hirarsa da manema labarai a jihar Bauchi, inda shugaban ya yi nuni da cewa, batar da burtaloli kasar nan ne Fulani makiyya komawa cikin jeji.
Sadikue ya bayyana cewa, hakan ya jano fulanin makiyaya suke yin kaura zuwa jeji a lokacin rani don su samu su ciyar da dabbobin su.
A cewarsa, amma a yau dabbobin na makiyya sun kasance suna yin kiwo a kan tituna wasu kuma suna kwana a cikin kwangaye.
“Hakan ya jano fulanin makiyaya suke yin kaura zuwa jeji a lokacin rani don su samu su ciyar da dabbobin su.”
Ya sanar da cewa, tun kafin zuwan turawa cikin kasar nan, akwai burtaloli da dabbobin makiyan ke bi, inda ya yi nuni da cewa, hatta wasu guaren da aka kebewa makiyyan wasu mutanen sun yi gine-gine akansu
Shugaban kungiyar ya bayana cewa, sai idan gwamnati ta dawo da burtulolin ne kamar yadda ake da su a jamhuriyya ta biyu a kasar nan, sannan za a samu sa’ida kan yawan samu rikece-rikice a tsakanin makiyya da manoma.
“Tun kafin zuwan turawa cikin kasar nan, akwai burtaloli da dabbobin makiyan ke bi, inda ya yi nuni da cewa, hatta wasu guaren da aka kebewa makiyyan wasu mutanen sun yi gine-gine akansu.”
Ya sanar da cewa, irin cin kashin da ake yiwa makiyya a kasar nan abin takaici ne, inda ya kara da cewa, da yawan su an kore su daga guraren da kakaknsu suke tun asali kusan sama da shakaru 100. duk shekara, ana yawan samu rikice-rikice a tsakanin manoma da Fulani makiyya a kasar nan.
A wani labarin kuwa, masana a fannin noman Rogo a kasar nan sun bayyana cewa, daga cikin tan miliyan 53 na Rogon da ake noma wa a Nijeriya a duk shekara, sama da kashi 90 a cikin dari ana sarrafa Rogon zuwa sauran wasu nau’ukan abinci.
A cewarsu, kiididdga ce ta tabbatar da wannan adadin, inda masanan suka kara da cewa, fannin na noman Rogon ya taimaka wajen samar wa da miliyoyin ‘yan Nijeriya aikin yi idan kuma aka inganta fannin, zai samar fiye da hakan.
Masanan sun sanar da hakan ne a a taron kara wa juna sani da suka gudanar a Babban Birnin Tarayyar Abuja, inda kuma suka yi nuni da cewa,kokarin da gwamtin tarayya ke ci gaba da yi na sake farfado noman na Rogo a Nijeriya, musamman kan daukain da Babban Bankin Nijeriya CBN ke samar wa a fannin, inda ya yi nuni da cewa, CBN ya bayar da gagarumar gudunawa wajen bunkasa fannin na noman Rogo a kasar nan.
“Kokarin na gwamtin tarayya ga fannin abin yaba wa ne matuka, musamman ganin cewa, nomansa na daya daga cikin amfanin gona da ke kara karfafa tattalin arzikin duniya”.
A cewar masanan, Nijeriya ce ke a kan gaba wajen noman Rogo, inda suka bayyana cewa, kasar na samar da kimanin tan miliyan 53 na Rogo a shekarar 2018 tare da kuma ta ke samar da akalla tan 7.7 ako wacce kadada daya, idan aka kwatanta da tan 23.4 da kuma tan 22.2 da ake samarwa a kasashen in Indonesiya da Thailand.
Masanan sun sanar cewa, ci gaba da sake farfado noman na Rogo a Nijeriya da gwamnati ke ci gaba da yi, musamman ta hanyar yin amfani da daukin da kan Babban Bankin Nijeriya ya kara taimaka wa matuka wajen kara bunkasa fannin na noman Rogon a kasar, da Kara fitar da shi zuwa kasuwar duniya, inda kuma hakan ya kara samar wa gwamnatin kasar kudaden shiga masu dimbin yawa.
“Nijeriya ce ke a kan gaba wajen noman Rogo, inda suka bayyana cewa, kasar na samar da kimanin tan miliyan 53 na Rogo a shekarar 2018 tare da kuma ta ke samar da akalla tan 7.7 ako wacce kadada daya, idan aka kwatanta da tan 23.4 da kuma tan 22.2 da ake samarwa a kasashen in Indonesiya da Thailand”.
Masanan sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi dukkan mai yuwa wajen kara samar da masu zuba jari a fannin na noman Rogon a kasar, musamman idan aka yi la’akari da irin dimbin kudaden shiga da fannin ke samar wa da manoman Rogon a kasar, inda kuma suka yi yi nuni da cewa, hakan zai kara taimaka wa wajen kara samar da ayyukan yi ga “yan kasar nan, musamman matasa.