Mafi yawan kwacen Facebook account da ake a yanzu, yana faru wa ne sakamakon yadda hackers suke turo sakonni a mutane ta messenger, suna cewa za su tura maka data 500gb kyauta.
To mutane kuma da son abu na kyauta, to ta wannan hanyar suke kwace wa mutane shafinsu na Facebook.
Suna cewa ne, turo min lambar wayarka zan turo maka 500gb kyauta. To zarar ka ga wani ya turo maka haka, ka yi sauri ka goge shi (blocking) daga cikin friends dinka, don hackers sun kwace Facebook account dinsa. Kar ka sake ka yi masa reply.
Yadda Zaka Gane Ko Wani Yana Amfani Da Shafinka Na Facebook
A takaice idan kana so kasan ko kuma yadda za ka gane idan wani yana amfani da shafinka na Facebook ba tare da sanin ka ba, to hakan yana faruwa ne, sakamakon mafi yawan lokuta mutane sukan sayar da wayoyin su ba tare da sun cire shafinsu na Facebook daga kan wayar ba. Wasu matsaloli suna iya biyo bayan hakan, kamar wanda ya sayi wayar ya ci gaba da amfani da shafin naka na Facebook, ya yi ta ‘Posting’ din duk abin da ya ga dama a ciki.
Idan hakan ko makamanciyar hakan ta faru, ga yadda za a warware matsalar cikin sauki.
Idan aka shiga ‘Settings’ za a ga ‘Security and Login’ a cikin sa akwai ‘where you’re Logged In’ a ciki za ka ga dukkan wayoyin ko ‘debice’ din da ake amfani da shafin naka na Facebook, sai ka shiga ‘Log Out of All session’ shikenan ka cire duk wani ‘debice’ ldin da ke amfani da shafin naka na Facebook.
Yadda Zaka Dakatar Da Yin Tagging Dinka A Facebook.
Mutane da dama suna koka wa a kan yadda mutane suke yawan ‘tagging’ dinsu a duk wani rubutu ko hoto da ake son isar da shi ga al’umma, kyakkyawa ko mummuna, wanda kuma shi wanda ake ‘tagging’ din nasa ba shi da bukatar hakan.
Tagging shi ne wani ya yi rubutu a shafinsa na Facebook, sai ya makala wasu daga cikin abokansa na Facebook din. Mafi yawan mutane basa son hakan, saboda bambamcin ra’ayi. Mutane daya wa sun rasa yadda za a yi su dakile hakan.
Hanya ma fi sauki da za ka iya magance wannan matsalar shi ne, idan ka shiga ‘Settings’ za ka ga ‘Timeline’ and ‘Tagging’ a ciki za ka ga abubuwa kamar haka:
– Timeline
– Tagging
– Review
Timeline
1. Who can post on my timeline?
Ma’ana, waye ka yarda idan ya yi Posting ya hau shafinka na Facebook?
A ciki za a baka zabi guda biyu:
– Friends (Abokai)
– Only Me (Ni kadai)
Sai ka zabi daya daga cikin biyun.
2. Who can see what other post on my timeline?
Ma’ana, waye ka yarda ya kalli rubutun da wani ya makala a shafinka na Facebook?
Shima idan ka shiga akwai zabi kamar guda biyar wadanda za ka zabi daya daga cikin su.
– Eberyone (kowa da kowa)
– Friends of my friends (abokan abokaina (matual friends)
– Friends (abokai)
– Friends edcept (abokai in banda…)
– Only me (ni kadai)
Sai ka zabi guda daya daga cikinsu.
3. Allow others to share your post to their story?
Ma’ana, ka ba da dama ga wasu su kai rubutunka zuwa akwatin labarinsu?
Shi kuma zabi biyu ake bayarwa:
– On (ka bada damar a kai rubutun naka)
– Off (baka bada damar a kai rubutun ba).
Tagging
1. Who can see posts that you’re tagged in on your timeline?
Ma’ana, waye zai iya ganin rubutun da wani ya makala a shafinka na Facebook?
A ciki za su baka zabi guda shida (6)
– Everyone (kowa da kowa)
– Friends of my friends (abokan abokaina (matual friends)
• Friends (abokai)
• Friends edcept (abokai in banda…)
• Specific friends (abokai na musamman)
• Only me (ni kadai)
Sai ka zabi wanda kake so a cikin su.
Review
1. Rebiew tags that people add to your posts before the tag appear on Facebook?
Ma’ana, ka duba rubutunka ko hoto da wasu suke so su dauka daga shafinka, su makala a shafinsu na Facebook?
Shi ma zabi biyu yake da shi:
• On (ka yarda)
• Off (baka yarda ba)
Sai ka zaba.
2. Rebiew posts that you’re tagged in before the post appear on your timeline?
Ma’ana, ka duba rubutun da wani ya makala a shafinka na Facebook, kafin ya bayyana a shafinka na Facebook?
Shima zabin biyu ne
• On (ka yarda)
• Off (baka yarda ba).
To idan ka zabi baka yarda ba, duk lokacin wani ya makala rubutunsa a shafinka na Facebook, ba zai hau shafinka na Facebook kai tsaye ba, sai Facebook din ya sanar dakai. Zai baka zabi ‘approbe’ ko ‘ignore’. Wato idan ka yarda sai ka yi approbed, idan kuma ba ka bukata sai ka yi ignored.