Da farko dai kafin ki fara kwalliyaakwai bukatar natsuwa, sannan akwai bukatar Lokaci, ina nufin wadataccen lokacin da zai isa a awaitar da kwalliya daki-daki kuma a tsare don tabbatar da cewar an yi kwalliyar a nutse bawai kawai a yi ta gara babu ba.
Don haka ki tabbatar duk abun da zai dauke maki hankali kin gama da shi. Abu na biyu kuma shi ne ki san yanayin fatarki tun daga launinta zuwa gautsi, tauri ko laushinta.
Wannan zai ba ki damar sanin ababen kwalliya da za ki harhada wadanda fustarki za ta karba. Saboda sau tari za ka gawasu sun yi kwalliya amma sam kwalliyar ba ta zauna a kan fatarsuba.
Ga yadda za ki gane yanayin fatarki:
Fata mai maiko (OILYSKIN): ko da yaushe za ki ga fatar jikinki tana da maiko ko kin shafa mai ko kirim ko ba ki shafa ba. Kuma da kin goge zuwa wani lokaci za ki ga fatar na nason maiko sannan kuma da kin yi kwalliya za ta narke ta lalace ki yi ta kyalli fauu.
Yadda Za Ki Kula Da Fata Mai Maiko (Oily Skin) Rika Yawan Yin Facial Mask Da Kwai: Yadda ake yin facial mask na kwai. Za ki fasa kwanki danye, sai ki cire kwan duwar ki bar farin, sai ki rufe fuskarki da tishu fefa (tissue paper), sai ki yi amfani da blusher (wani burushi na shafakayan kwalliya) ki na dangwala rruwan kwan kina shafawa a tishu fefar da ki ka lullube fuskarki da ita har sai kowane bangare nafuskar ta ki ta jike da ruwan farin kwan, za ki bar shi na tsawo nmintuna 10 zuwa 15 sai ki wanke da ruwan dumi.
Hanya ta biyu na magance maikon fuska ita ce yawan gogefuskarki da lemon zaki ko lemun tsami kafin shafa kayan kwalliya. Yana da kyau ki san cewa yin amfani da nikakkiyar farar shinkafa ki jika ta cikin madara kana ki cuda kafatanin jikink ida ita akalla mintina 20 kafin ki shiga wanka ba wai kawai magance maikon fuska ya ke ba, a’a, hadin na sanya laushi da shekin fata.
A kula in ki ka yi wannan hadin ba kya bukatar wanka da sabulu, sai dai akwai bukatar ki yi amfani da ko dai ruwan sanyi ko na dumi wajen dirje jikinki da kyau ta yadda kwabin zai wanku sosai.
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kaimu