Jama’a assalamu alaikum, barkanmu da wannan lokaci na sanyi. Da fatan Allah ya nuna mana karshensa lami lafiya, amin.
Lokacin sanyi wani yanayi ne da ke zuwa da nau’i daban-daban. Sanyi ko hunturu kamar yadda aka sani lokaci ne da yake bukatar kulawa dari bisa dari, musamman ma ga yara.
Iyaye musamman iyaye mata akwai wani nauyi na musamman da ya rataya a kansu lokacin hunturu inda za mu ga cewar ko babba ne sanyi na masa illa balle kuma yara kanana wadanda ba su san yadda za su kula da kansu ba.
Ga wasu daga cikin hanyoyi da za mu bi don kulawa da yaranmu lokacin sanyi:
- Iyaye musammam uwa ta tabbatar ta samar wa yaranta kayan sanyi irin su hula, rigan sanyi da kuma dogon wando dogo.
- Kanana yara irin jarirai yana da kyau a samar musu pampas wanda zai taimaka wajen tare jikewar kaya wanda hakan zai taimaka sosai don hana yara kamuwa da cutar sanyi irin su Mura, tari da kuma sauran cuttuka da hakan ka iya haifarwa.
- Â Masu fitsarin kwance a wannan fannin ana so uwa ta zama mai sa ido sosai, da kuma hakuri da juriya domin kuwa idan uwa ba ta da hakuri da juriya to yaranta sun yi ta kamuwa da cuttukan da ke tattare da sanyi kenan. Idan yaro ya yi fitsari ana so uwa komai dare ta tashi ta canza masa kaya da kuma shimifida saboda rashin yin haka na iya cutar da lafiyar yara.
- Ya’ya mata ana so uwa ta kula sosai wajen kare lafiyar yaranta musammsn `ya’ya mata. Rashin saka dankwali ga ‘ya mace ka iya haifar da illoli daban-daban ga lafiyarta. Rashin saka dankwali musamman lokacin sanyi yana iya haifar da matsanancin ciwon kai da kuma cutar mura da tari ga ‘ya mace.
Iyaye sai mu kula.