Kamar yadda kowa ya sani Nijeriya za ta gudanar da babban zaben shugaban kasa na 2023 a gobe Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023 wanda ake sa ran jam’iyyu 18 za su shiga a dama da su.
Zaben wanda ake tunanin zai fi zabi a tsakanin jam’iyyar APC da ke mulki a kasar nan, da PDP, NNPP da jam’iyyar LP a matsayin manyan masu adawa da suke neman kujerar shugaban kasa da sauran kujeru ruwa a jallo hadi da wasu jam’iyyun.
- APC Ta Soki Sabon AIG Da Kwamishinonin ‘Yansanda 4 Kan Ziyartar Wike
- Da Dumi-Dumi: Sergio Ramos Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sifaniya Kwallo
Bayan zaben shugaban kasa za a yi zaben ‘yan majalisun tarayya dukka a wannan ranar ta Asabar.
Nijeriya dai na da mazabun jefa kuri’a 176,846 a fadin kasar nan, amma za a gudanar da zaben 2023 ne a mazabu 176,606 sakamakon cewa guda 240 ba su da rijistan masu zabe a cewar INEC.
Sai dai, masana na kallon zaben 2023 kamar zai sha banban da sauran zabukan da al’umma suka saba yi a kasar nan lura da cewa ana tunanin gudanar da zaben cikin gaskiya kuma sahihi ta hanyar amfani da wasu tsaruka da shirye-shiryen da ake ganin za su hana sayen kuri’u balle a juya wa mutane ra’ayin zabin wani ko wasu don kudi ko don wani abun na daban.
Kazalika, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bada tabbacin gudanar da sahihin zabe ta hanyar amfani da wani na’urar tantance masu zabe gabanin jefa kuri’a wanda ta hakan za samu raguwar magudi da kakaba wa mutane wanda basu so.
Idan aka yi la’akari da zabukan baya da aka gudanar a kasar nan za a iya fahimtar yadda wasu ke kokonto sahihancin zabuka bayan an kammala gudanar da su, hatta zaben baya-bayan nan da aka gudanar a 2019 wasu na da korafin an yi magudi amma dai haka lamarin ya tafi.
A bisa hakan mun zanta da wani masharhancin lamuran yau da gobe, Dakta Adamu Ibrahim Gambo, inda ke mai nuni da cewa, “Za mu iya cewa da yiyuwar da fatan za a gudanar da zaben da ba a taba yin irinsa ba a 2023, don muna kyautata zagon zaben 2023 zai kasance wanda al’umma suka zaba ne zai samu damar dakilewa karaga. In ka yi la’akari da cewa, a zabukan baya, za ka lura ana amfani da kudade gabanin ko lokacin zabe wajen sayen kuri’a a hannun jama’a; to a daidai wannan lokacin na wannan zaben babu irin wadannan kudaden da za a je a sayi kuri’un talakawa. In ma akwai gaskiya ba lallai ya yi tasiri irin yadda aka saba a kasar nan ba.
“To, abun takaicin shi ne, ba wai wannan tsarin ne ya kamata a ce ana lura ma da shi a kasar nan ba, kamatuwa ya yi a ce al’ummar kasar mun canza kanmu da kanmu ne wato cigabanmu ya kai ba sai wai an bamu kudi kafin mu zabi mutum ba; idan ya zama dole sai an yi hakan ne, zai zama kowani lokacin zabe shugaban da ke kokarin barin gado zai so yin koyi da wannan tsarin na sauyin kudi ko wani tsarin da ka iya illa ma al’umma ta wani fuskar. Don haka akwai bukatar mu cire sai an biya mu kafin mu zabi mutu, ta haka ne za mu zabi shugaban da muke so wanda kuma dole ya mana aiki don ba sayen kuri’nmu ya yi ba.”
Masanin ya kuma kara da cewa, batun tsaro da ake tunanin ka iya kawo barazana ga zaben zuwa yanzu mutane sun gamsu ba zai haifar da wani matsala ga zaben ba lura da cewa an samu saukin matsalolin tsaro a halin yanzu. Sai dai ya koka kan yadda jama’a za su iya shan wahalar zirga-zirga a yayin zaben sakamakon wahalar samun Mai a halin yanzu.
Ya cigaba da cewe, “Idan ka yi nazarin halin da ake ciki, za a iya cewa akwai fatan cewa ba za a yi rigima sosai a yayin zaben ba, ka san kudi na daga cikin abun da ke sanya matasa fita hayyacinsu har su je yi ta fada a tsakaninsu da yin bangar siyasa. To wannan karancin kudin zai iya zama mafita ga wannan damuwar koda kuwa ba a daina dukka ba, amma zai iya ragewa, kodayake fata mu yi amma komai zai iya canzawa domin ‘yan siyasar nan ba su da tabbas.”
A gefe daya, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ce, karancin kudi da ake fuskanta zai zama barazana ga zaben ba domin akwai wadatattun takardun kudi a hannunta da za ta iya gudanar da aikin zaben da ke gabanta cikin kwanciyar hankali. Bayan wadatattun kudaden, INEC ta ce, tana da wadatattun kayayyakin aiki wajen gudanar da zaben.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu shi ne ya shaida hakan a lokacin da ziyarci gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, ya ce, su INEC suna bukatar kudi kash dinta ba wai a tura musu ta banki ba domin gudanar da ayyukan da ke gabansu.
Ya yi bayanin cewa duk da cewa wasu kudaden za su biya masu hakkin ne ta hanyar taransifa amma akwai wasu ayyukan da kash ne za a biya su.
Ya bada misali da irin ayyukan fusuri da zirga-zirga dole za a biyasu ne ta hanyar kash, da kuma wasu ayyukan gaggawa da ka iya bijirowa wa hukumar.
Wakilinmu ya nakalto cewa kudaden da INEC take bukata domin gudanar da zaben, an aike da su ga kwamishinonin da za su kula da ayyukan zaben a jihohin kasar nan kai tsaye, inda wasu kwamishinonin tunin suka tabbatar da cewa CBN ya tura musu kudin.
Wakilan Jam’iyyu (Agents) 1,574,301 Ne Za Su Yi Aikin Zaben 2023
INEC ta sanar da cewa adadin wakilan jam’iyyun siyasa su miliyan 1,574,301 ne za su sanya ido wa jam’iyyunsu 18 a yayin babban zaben 2023 da ke tafe.
A taskar bayanan wakilan da INEC ta fitar a ranar Litinin ta nuna cewa jam’iyyar PDP ce ke da mafi rinjayen wakilai har guda 176,588.
Kazalika jam’iyyar APC tana da wakilai 176,233; sai kuma New Nigeria Peoples Party (NNPP) mai wakilai 176,200; ita kuma Labour Party LP tana da 134,874.
Sannan, dukkanin jam’iyyun sun kuma zabi jami’an sanya ido na tattara sakamakon zabe su 68,057 da Agents 27 da za su kasance a babban cibiyar tattara sakamakon zabe a matakin kasa domin sanya ido.
A bangaren tsaro kuwa, hukumomin tsaro sun tabbatar da kyautata lamuran tsaro a yayin zaben 2023 domin tabbatar da an gudanar cikin koshin lafiya.
Shugaban hukumar tsaro ta kasa, Janar Lucky Irabo shi ne ya bayar da tabbacin a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a Abuja inda yake baiwa ‘yan kasa tabbacin kokarin sojoji na ganin an yi zaben cikin koshin lafiya.
Ya gargadi masu mummunar aniya da cewa kada su kuskura su yi kokarin haifar da rashin da’a ko rashin tsaro domin ba za su samu gurbin hakan ba, yana mai cewa jami’an tsaro ba za su bari wani ya nemi kawo tsaiko ga zaben ba.
Irabo wanda ya yi wata ganawar sirri da shugaban sojin kasa, shugaban sojin sama da na ruwa, da sufeto janar na ‘yan sanda, darakta janar na hukumar tsaron farin kaya da na NIA hadi da na saura, inda suka tattauna yadda za su tabbatar da tsaro a yayin zaben.
Zaben nan dai za a fafata ne tsakanin manyan ‘yan takara da suka hada da Bola Ahmed Tinubu da ya fito daga shiyyar Kudu, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya fito daga shiyyar arewa maso gabas, shi kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP, ya fito ne daga shiyyar Arewa maso yamma asalin dan jihar Kano, yayin da shi kuma Peter Obi na jam’iyyar LP shi ma ya fito daga shiyyar Kudu yayin da kowa ke neman dalewa karagar mulkin shugabancin Nijeriya.