Ranar Asabar da ta gabata ce, kungiyar masu sana’ar maganin gargajiya ta kasa ta gudanar da zaven shugabanninta na kasa waxanda za su tafiyar mata da harkokinta na shekaru huxu masu zuwa a xakin taro na otal din Kariya a karamar hukumar Karu na Jihar Nasarawa.
A shekaru 35 na kafa kungiyar, wannan shekarar ce aka zabi shugabannin kungiyar a kan tsarin zabe wanda kowa zai yi murna kan matakin da aka xauka na yin hakan, shekarun da suka gabata a kan yi nadi ne kawai.
Kafin a gudanar da zaven, sai aka bai wa ‘yan takarar mukaman mintuna, inda suka yi wa mabobinsu jawabi a kan abubuwan da za su yi wa ‘yan kungiyar da kuma kungiyar domin samun ci gaba da kowa zai ce sam barka.
Dan takarar muqamin mataimakin shugaban qungiya na Arewa ta tsakiya,
Dakta Baba Audu Boka ya yi wani jawabi wanda ya burge mambobin da ke cikin xakin taron, inda ya ce idan aka zave shi a muqamin zai rika ilmintar da matasa abubuwa daban-daban dangane da maganin gargajiya.
An zabi mutane 23 waxanda za su jagoranci harkokin kungiyar na shekara hudu, da suka hada da Dakta Kabir Muhammed Naborgu a matsayin Shugaban kngiyar, Dakta Okpara Chigozie mataimakin a matsayin mataimakin Shugaban kungiyar, Honorabul (Dr) Abu Huraira Juwadu a matsayin Sakataren kungiya, Dakta Sani Bin Abdullahi a matsayin mai kula da jin dadin ‘yan kungiya, Dakta Goni Ali Hassan a matsayin mataimakin Shugaban kungiyar na Arewa maso gabas, Dakta Ishak Haruna a matsayin Sakataren tsare- tsare, Dakta Fatimatu Yakubu a matsayin Shugabar mata ta Arewa, Dakta Hashiru Halilu a matsayin mataimakin Shugaban kungiyar na Arewa maso yamma.
Sauran sun hada da Dakta Hadiza Ibrahim a matsayin Shugabar mata Arewa ta tsakiya, Dakta Jabbi Muhammed Bawa a matsayin Ma’aji na kungiyar, Dakta Nancy Chinyere a matsayin shugaban kungiyar ta Kudu maso gabas, Dakta Sa’adatu Isma’ila Haruna a matsayin Sakatariyar harkokin kudi, Dakta Nasiru Kaduna a matsayin mai tsawatarwa na kungiyar. Sauran sun hada da Honorabul (Dr) Abubkar Usman a matsayin mai binciken yadda aka kashe kudi, Dakta Baba Audu Boka a matsayin mataimakin shugaban kungiyar na Arewa ta tsakiya, Dakta Abubakar Tahir a matsayin Darektan ayyuka da horarwa, Dakta Abdullahi Idris Muhammed a matsayin Darekan bincike, Dakta Hassan Baba a matsayin mai tsawatarwa, Dakta Adamu Ningi a matsayin shugaban ‘ya’yan kungiya, Dakta Shafi’u Sardaunan Garu a matsayin jakadan kungiya, Dakta Sani Garba NCP, Dakta Ibrahim Abdul a matsayin Jami’in hulda da jama’a.