Zaki ya halaka mai ba shi abinci har lahira a yayin ciyar da shi a wurin nazarin dabbobi da ke jami’ar Obafemi Awolowo a Ile-Ife na Ibadan na Jihar Oyo.
Mutumin mai suna Mista Olabode Olawuyi, ya kwashe shekara tara yana ciyar da wannan zaki, ya kasance mai kula da dabbobin na tsawon shekaru aru-aru.
- Amurka Ta Zama Babban Cikas Ga Dakile Yakin Gaza Bayan Da Ta Hau Kujerar Na Ki
- Shugaban Faransa Ya Gana Da Wang Yi
Mai magana da yawun jami’an, Abiodun Olarewaju, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce, “Mista Olawuyi shi ne yake kulawa da zakin tun lokacin da aka haifeshi a jami’an tsawon shekaru 9 da suka gabata, sai dai kula abun takaicin zakin ya kashe wannan mutumin ne lokacin da yake kokarin ciyar da shi.
“Sauran ma’aikatan da lamarin ya faru a gaban idanunsu sun yi kokarin ceto mutumin, amma zakin ya ci karfinsu wanda ya raunata su har yayi sanadiyyar mutuwarsa.”
Olarewaju ya kara da cewa lokacin da aka samu wannan mummunan labarin, mahukunata makarantar karkashin shugabancin, Farfesa Adebayo Bamire suka katse ganawar da suke yi domin zuwa wurin da lamarin ya faru.