Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Geoffrey Uche Nnaji, ya yi murabus daga majalisar ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sakamakon zargin jabun takardar shaida da aka yi masa.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin bayani da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya tabbatar da murabus din a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Shugaban Kasa ya amince da murabus din “cikin natsuwa da sadin rai.”
- Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
- Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0
Dambarwar Nnaji ta fara ne bayan kafar labarai ta Premium Times ta wallafa sakamakon binciken da ta gudanar game da zargin jabun takardar shaidar karatun Nnaji.
Wata kafar labarai daban, Peoples Gazette, tun da farko a shekarar 2024, ta ruwaito labaran da ke zarginsa da yin jabun takardar shaidar NYSC.
Sai dai Nnaji ya karyata labarin da Premium Times ta wallafa, yana mai cewa zargin aiki ne na abokan hamayyar siyasa a Jiharsa ta Enugu.
Tsohon ministan, wanda aka nada a watan Agusta 2023, ya mika takardar murabus dinsa a ranar Litinin ga Shugaban Kasa, inda ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta yi wa kasa hidima.
A cikin wasikar tasa, tsohon ministan ya bayyana cewa ya zama abin kai hare-hare na “tsananin batanci” daga abokan hamayyar siyasa da ke neman bata masa suna.
“Ina gode wa Shugaban Kasa bisa amincewa da ni da kuma damar da ya ba ni na bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa,” in ji Nnaji, yana mai kara da cewa yana janyewa ne don kare mutuncin gwamnatin.
Shugaba Tinubu, yayin da ya amince da murabus dinsa, ya yaba wa Nnaji bisa hidimar da ya bayar ga kasa tare da yi masa fatan alheri a harkokinsa na gaba.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa matsin lamba na karuwa kan ministan bayan da jami’ar Unibersity of Nigeria, Nsukka (UNN) ta nesanta kanta daga takardar shaidar da ake zargin Nnaji ya gabatar.
A cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 2 ga Oktoba, 2025, wadda Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfa Simon Ortuanya, ya sanya wa hannu, jami’ar ta bayyana cewa bayanan da ke hannunta sun nuna cewa Nnaji, mai lambar shigar makaranta 1981/30725, an karbe shi a shekarar 1981 domin karatun Microbiology/Biochemistry, amma bai kammala karatunsa ba.
“Saboda haka, Jami’ar Nijeriya, Nsukka ba ta taba bayar da takardar shaidar da ake ikirari a watan Yuli 1985 ga Mista Geoffrey Uchechukwu Nnaji ba, kuma ba za ta iya bayar da ita ba,” in ji jami’ar.
Jami’ar ta ce wannan matsayi nata ya yi daidai da abin da ta bayyana a cikin wata wasika da ta aike wa Hukumar Karbar Korafe-korafe ta Jama’a a ranar 13 ga Mayu, 2025, a matsayin amsa ga irin wannan tambaya da aka yi a baya.
Sai dai a cikin takardarsa da ya gabatar gaban kotu, Nnaji ya amince cewa har yanzu bai karbi takardar shaidar digirinsa daga jami’ar ba, inda ya danganta jinkirin da abin ya samu ga abin da ya kira “rashin hadin kai” daga jami’an UNN.
Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa ba za ta dauki mataki kan lamarin ba saboda shari’ar tana gaban kotu.
Sai dai, Cif Uche Nnaji ya riga ya karyata zargin jabun takardar shaidar karatu da aka yi masa, inda ya nemi hukumar jami’ar da ta saki takardar shaidar karatunsa.
A yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, ministan ya bayyana cewa zargin jabun takarda na da tushe na siyasa, kuma an tsara shi ne da nufin bata masa suna kafin zaben gwamna na 2027 a jiharsa.
A halin yanzu, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsara ranar 10 ga Nuwamba domin sauraron karar da Minista Nnaji ya shigar kan Jami’ar UNN.
Ministan ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1909/2025 ne sakamakon zargin jabun takardar shaida da aka yi masa.