Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya samu ‘yanci daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja a yammacin yau Juma’a, bayan ya cika sharuɗan belin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta gindaya masa.
Kakakin hukumar gidan gyaran hali na babban birnin tarayya, Adamu Duza, ne ya tabbatar da sakin Bello a yammacin yau Juma’a.
- Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kara Wa Hukumar NEPC Kudaden Aiki
- EU Ta Ware Euro Miliyan 1 Don Tallafa Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Da Kwalara Suka Shafa A Nijeriya
Idan za a iya tunawa, a ranar Alhamis ne babbar kotun ta bayar da belinsa bisa sharuɗi, ciki har da biyan kuɗi naira miliyan 500.
Mai shari’a Maryann Anenih ce ta yanke wannan hukunci a shari’ar da ake yi masa kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati.
Kotun ta gindaya cewa Yahaya Bello ya kawo mutane uku da za su tsaya masa, waɗanda za su kasance masu mallakar kadarori a manyan wuraren Abuja, kamar Guzape, Wuse 2, Apo, Asokoro da Jabi.
Har ila yau, waɗanda za su tsaya masa dole ne su gabatar da hotunan fasfo guda biyu tare da ingantacciyar shaida ta ɗan ƙasa (NIN).
Bugu da ƙari, kotun ta umarci tsohon gwamnan da ya ajiye fasfo ɗinsa da duk wasu takardun tafiye-tafiye a ofishin rajistar kotun, don tabbatar da cewa ba zai bar ƙasar ba ba tare da izini ba.
Tun farko, Mai shari’a Anenih ta ƙi amincewa da buƙatar belinsa na farko, amma ta bayar da belin sauran waɗanda ake zargi tare da shi a shari’ar.
Duk da haka, a ƙarshe an ba shi beli bayan cika duk sharuɗan da kotun ta gindaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp