Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya ta Ƙasa (NANS), ta bai wa Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), wa’adin kwanaki bakwai don su warware rikicin da ke tsakaninsu.
Shugaban NANS, Olushola Oladoja ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
- 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa
- Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara
Ya nuna damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ƙamari tsakanin gwamnati da ASUU, yana mai gargaɗin cewa ɗaliban Nijeriya ba za su lamunci tsayawar karatu ba sakamakon yajin aiki.
Oladoja, ya ce an samu shekaru biyu ana karatu ba tare da yajin aiki ba a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba, abin da bai taɓa faruwa tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999 ba, sai dai, barazanar sabon yajin aikin da ASUU ke yi yanzu na iya barazana ga wannan ci gaba.
Shugaban NANS ɗin ya yaba da tsare-tsaren ilimi na Shugaba Tinubu, tare da lissafa wasu daga cikinsu kamar kafa Asusun Lamunin Dalibai (NELFUND), da cire ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’i daga tsarin IPPIS, da kuma soke tsarin tura kashi 40 na kuɗaɗen shiga zuwa gwamnatin tarayya, da a tallafin musamman daga TETFund.
Amma ya nuna damuwa cewa jinkiri wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta yi da ASUU na ƙara haifar da rashin jituwa.
Ya roƙi Shugaba Tinubu, da ya sa baki kai-tsaye don kawo ƙarshen rikicin, yana mai gargaɗin cewa jinkiri wajen ɗaukar mataki na iya gurgunta ci gaban da aka samu a fannin ilimi.