Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da tallafin motocin sufuri kyauta ga duk daliban da ke sha’awar komawa makarantu Arewacin kasar nan don ci gaba da da karatu bayan kare yajin aikin ASUU.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakatariyar Yada Labarai ta Ma’aikatar Ilimi ta Jami’ar, Misis Mansurat Amuda-Kannike, ta fitar ranar Talata a Ilorin.
- An Tsaurara Tsaro A Abuja Bayan Gargadin Harin Ta’adanci
- Sabon Ci Gaban Sin Zai Samar Da Sabbin Damammaki Ga Kasashen Duniya
Amuda-Kannike, ta ce matakin ya biyo bayan dakatar da yajin aikin ASUU na tsawon watanni takwas da ta shita.
Ta ce kwamishinan, Dakta Alabi Abolore, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ta fito da wata hanya don fadada romon dimokuradiyya ga daliban Kwara da ke manyan makarantun kasar nan.
“Daliban da abin ya shafa ana ran za su bayyana don takaitace su a ranar da za su koma makarantunsu a ma’aikatar ilimi ta manyan makarantu a ranar Asabar, 29 ga Oktoba da karfe 6:30 na safe.
“Har ila yau, ma’aikatar tana gab da kammala bayar da tallafin a lokacin da aka bude rajistar masu son cin gajiyar ta yanar gizo,” in ji ta.