Taron da aka yi a yammacin ranar Talata tsakanin shugabannin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da gwamnatin tarayya, an tashi ba tare da cimma wata matsaya ba.
Hakan na nufin yajin aikin da malaman jami’o’in ke yi zai ci gaba bayan shafe wata shida ba tare da samo bakin zaren matsalar ba.
- Manchester United Ta Amince Ta Raba Gari Da Ronaldo A Bana
- Ku Tuhumi PDP Kan Yajin Aikin ASUU – Keyamo Ga ‘Yan Nijeriya
Malaman sun gana da kwamatin Farfesa Nimi Briggs a ranar Talata a Hukumar Jami’a ta Kasa da ke Abuja tare da fatan ganin an shawo kan matsalar.
Wani jigo a ASUU da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa LEADERSHIP, cewa mambobin kwamitin sulhu na Briggs ba su zo da wani sabon tayi kan teburin sulhun ba.
A maimakon haka, majiyar ASUU ta ce, kwamitin ya roki malaman da su dakatar da yajin aikin da suke yi, tare da yin alkawarin cewa za a sanya damuwarsu a cikin kasafin kudin 2023.
Majiyar ta ce taron wanda aka fara shi da misalin karfe 12 na rana, ya shafe kusan sa’o’i uku ba tare da cimma matsaya ba.
Yajin aikin ASUU na ci gaba da zama babbar barazana ga bangaren ilimi.
A baya-baya nan kungiyar kwadago ta kasa (NLC) tare da wasu kungiyoyin ma’aikata sun goya wa ASUU baya wajen yin zanga-zangar ganin an kawo karshen takaddamar yajin aikin.
Amma har yanzu shiru kake ji malam ya ci shirwa.