Wani malami a Jami’ar Tarayya da ke Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi, Dakta Auwal Mustapha Imam, ya yi barazanar ajiye aikinsa matukar gwamnati ta ki biyan malamai albashinsu na watanni da suke bi tun bayan tsunduma yajin aikin ASUU.
Ya bayyana hakan ne a hirarsa da LEADERSHIP Hausa, Inda ya ce shi ne kadai malamin da yake da digiri uku a duk tsangayar, inda ya sha alwashin barin aiki a Jami’ar matukar ba a biya shi albashinsa na watannin baya ba.
- Zan Mayar Da Jami’o’i Karkashin Kulawar Gwamnatocin Jihohi Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku
- ‘Yan Daba Sun Tarwatsa Taron Gangamin Takarar Atiku A Ribas
A cewarsa, malamai masu yajin aikin sun cancanci a biya su albashinsu na watannin da suke yajin aiki, inda ya yi ikirarin cewa duk da sun rufe azuzuwa amma suna yin bincike na ilimi da kuma duba kundin daliban da ke shirin kammala digiri saboda haka sun cancanci a basu albashi.
Ya ayyana matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na kin biyansu albashi don sun tafi yajin aiki a matsayin mugunta.
“An saka mu cikin wahala da gangan, muna cikin talauci. Mutane na cikin bashi da matsaloli iri-iri. Akwai wadanda a cikinmu motar haya suka koma tukawa, wasu sun sayar da motocinsu. Rashin kyautawa ne, zalunci ne gwamnati ta ce ba zata ba da wannan kudin ba” Inji shi.
Malamin ya ci gaba da cewa akwai ire-irensa da yawa da zasu bar aikin, su nemi wasu wuraren da za a mutunta su muddin aka ki biyansu albashin watannin baya.
Imam ya jaddada cewa sun tafi yajin aikin ne domin kubutar da ilimin jami’oi kada ta lalace kamar yadda gwamnati ta lalata makarantun firamare da sakandare a cewarsa.
Babban malamin, ya ce daya daga cikin abubuwan da suke bukata daga gwamnati shi ne a ba jami’oi damar yin amfani da kudadensu na shiga.
Ya ce jami’oi suna amfani da kudadensu wajen biyan wasu malamai daga wasu wurare saboda karancin malaman jami’a a kasar nan, inda ya yi nuni da cewa muddin ba a ba su ‘yancin cin gashin kansu ba game da kudadensu, to, ba za su iya daukar malaman haya ba don cike gurbin rashin isassun malamai na dindindin a makarantunsu.