Gwamnatin tarayya ta nemi afuwar dalibai da iyaye bayan da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta janye yajin aikin watanni takwas.
Kungiyar ASUU ta sanar da dakatar da yajin aikin a ranar Juma’a.
- Za A Gudanar Da Babban Taron Wakilan JKS Karo Na 20 A Ranar 16 Ga Wata
- Bunkasar Kimiya Da Fasahar Sin Ba Kawai Zai Amfani Jama’arta Kadai Ba Ne Har Da Al’ummar Duniya
Yanzu haka dai ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta mika godiya ga duk wadanda ke da hannu a tattaunawar da ta kai ga janye yajin aikin.
Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Olajide Oshundun ya fitar, ta ce a bangare guda: “Yanzu da ASUU ta yanke shawarar yin biyayya ga hukuncin kotun masana’antu ta kasa ta janye wannan yajin aikin, muna neman afuwar dukkan dalibai da iyaye, game da wannan yajin aikin da aka dade ana yi ba bisa ka’ida ba, wanda ba shi da tushe balle makama.”
Ya kara da cewa “ana aza harsashin ginin da muke da yakinin zai ceci ‘yan Nijeriya, wannan abin da aka so ba ne.”