A ranar Talata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a halin yanzu makaman da ake amfani da su a yakin da ake tafkawa a tsakanin kasar Rasha da Yukrain sun fara shigowa yakin tafkin tekun Chadi, inda daga na za su bazu zuwa sauran kasashen Afrika, wanda hakan zai cigaba da kara wutar mastalar tsaron da ake fuskanta a yankin.
Ita dai yankin kogin Chadi yana da dinbin albarkan tattalin arziki ya kuma hada yankunan Yammaci da Tsakiyar Afrika da suka hada da kasashen Cameroon, Chadi, Nijar da Nijeriya.
- 2023: Muradun CAN Da Na Dattawan Arewa A Sikeli
- Shugaban Rikon Kwarya Na Chadi Na Son Zurfafa Hadin Gwiwa Tare Da SinÂ
Shugabga Buhari ya yi wannan bayanin ne a yayin bude babba taron shugabannin kungiyar kasashen yakin tafkin kogin Chadi a karo na 16 da aka yi a babban dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kasa wanda kuma shi ne shugaban kungiyar, ya ce, yakin na Rasha da Yukrain ya kara haifar da bazuwa kananan makamai a sassan duniya wanda hakan kuma ya karfafa kirar bukatar a kara tabbatar da tsaro a iyakokin kasashen yankin don katse yiwuwar shigowar makamai daga wadannan yankin.
Daga nan shugaban kasa Buhari ya kuma kara bayyana cewa, rikicin kasar Rasha da Yukrain da saura yankunan da ke fuskantar tashe-tashen hankula suka bunkasa harkokin ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Yammacin Afrika.
Ya ce, duk da kokarin da ake yi na rage karfin ‘yan Boko Haram, har yanzu kungiyar na nan na cigaba da ayyukanta na ta’addanci.
“Ina farin cikin sanar da ku cewa, akan wannan shawarar muka karfafa ayyukan rundunar hadin gwiwa na MNJTF inda suka gudanar da aikinsu cikin nasara ta hanyar gabatar da rukunin aikin fafatawa har sau uku da aka sa wa suna kamar haka ’Ops‘YANCIN TAFKI (I&II) da ‘Ops Lake Sanity I’ da kuma ‘Ops Lake Sanity II’, za kuma a shirya mataki na gaba ne bayan tattara bayanai da darussan da aka cimma a shirye-shiryen mu na baya.
“Ina ma farin cikin sanar da ku cewa a yayin gabatar da farmakin ‘Ops Lake Sanity I’ an samu nasarar kashe mayakan Boko Haram da dama.
“ya za dole mu kwana da sanin cewa, duk wadanna nasarorin da kungiyar MNJTF ta samu a kan ‘yan ta’addan har yanzu akwai barazanar ‘yan ta’adda a wasu yankunanmu.
A nasa jawabin, babban sakataren hukumar LCBC, Ambasada Mamman Nuhu, ya sanar da cewa, Nijeriya ta biya kasonta na Dala 209,075,748 don tafiyar da rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga shekarar 2015 zuwa 2021.
Taron ya samu halartar shugabanni 6 na kasashen kungiyar in banda shugaban kasa Cameron, Paul Biya wanda ya samu wakilcin daya daga cikin ministocinsa.
Shugabannin kasashe da suka samu hakarta sun hada da Farfesa Faustine Archange TOUADERA, na Jamhoriyya Afrika ta Tsakiya; Mohamed BAZOUM, na kasa Nijar; Patrice TALLON, na jamhoriyyar Benin; Mahamat Idriss Deby ITNO, na kasar Chad da Mohamed AL-MENFI, na kasar Libya.