Babban Lauya mai mukamin (SAN), Mista Yakubu Chonoko Maikyau, ya samu nasarar zama sabon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA).
Maikyau ya samu nasarar ne a zaben da NBA ta gudanar da karfe 12 na safiya zuwa zuwa karfe 11.59 na daren ranar Asabar.
- CDD Ga INEC: Ku Dabbaka Sahihin Zaben Da Kuka Yi A Osun, Ekiti A 2023
- Tarayyar Turai Za Ta Yi Nazari Kan Lafta Wa Rasha Karin Takunkumai
Ya samu nasarar ne bayan samun kuri’u 22,342 da hakan ya kai shi ga kada ‘yan takara biyu wato Messrs Joe-Kyari Gadzama (SAN), shugaban kwamitin tsaro na NBA da kuma tsohon sakataren Janar na NBA, Jonathan Taidi.
Kamar yadda shugaban kwamitin zaben NBA, Ayodele Akintunde (SAN), ya sanar a taron manema labarai ya ce masu zabe 59,392 ne suka yi rajistar zaben yayin da kuma sama da masu zaben 3,000 suka gaza samun dama bisa gaza tantancesu.
Ya kara da cewa, mutum 34,809 ne suka kada kuri’ar kwatankwacin kaso 58.61 na adadin wadanda suka dace su yi zaben.
Ya ce Maikyau ya samu kuri’u 22,342 kwatankwacin kaso 64.6 cikin dari na wadanda suka kada kuri’ar da hakan ya ba shi damar shiga ofishin Shugaban NBA na kasa.
Ya kuma ce, Gadzama SAN ya samu kuri’u 10,842 yayin da kuma Taidi ya samu kuri’u 1,380 kacal.
Kazalika wakilinmu ya nakalto cewa, Adesina Adegbite ya zama sakataren Janar na NBA yayin da kuma Daniel Ka-Ayli ya zama mataimakin sakataren janar.
Chinyere Obasi kuma aka zaba a matsayin Sakataren walwala da jin dadin mambobin NBA na kasa, sai kuma Habeeb Lawal ya zama sakataren watsa labarai, Olawole Ajiboye ya zama mataimakin sakataren watsa labarai sai kuma Anze-Bishop Ladidi ya zama mai rike da lalitar NBA wato ma’aji.
Kungiyar lauyoyin ta kuma zabi Linda Bala a matsayin mataimakin shugabar kungiyar na 1 da kuma zabin Clement Ugo mataimakin shugaban na 2 da Amanda Demechi-Asagba mataimakin shugaban NBA na 3.
Kazalika NBA ta zabi Lauyoyi 20 a matsayin mambobin majalisar kolinta da da su wakilci shiyyoyin Yammaci, Gabashi da Arewaci a fadin kasar nan.
Da ya ke jawabin amsar ragamar mulkin NBA, Barista Yakubu SAN ya nemi hadin kan dukkanin mambobin kungiyar da su dafa masa domin Kai kungiyar zuwa ha tudun mun-tsira.
Ya ce zai tabbatar da walwalwarsu da jin dadinsu gami kuma da kare musu kima da mutunci a kowani lokaci domin saukaka musu yanayin aiki a fadin kasar nan.