Mai ba gwamnan jihar Katsina shawara kan harkokin siyasa, Hon. Yau Umar Gwajo-Gwajo, ya yi kira ga ‘yan adawa da su zo a yi gwamnati domin ci gaban al’ummar jihar Katsina baki ɗaya.
Hon. Ya’u Gwajo-Gwajo ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai jin kaɗan bayan shigarsa sabon ofis na mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa.
Tsohon Kakakin Majalisar dokokin ya ce, in dai da gaske adawa ake yi, to yana kira da babbar murya da su zo a haɗa kai a ciyar da jihar gaba domin duk abinda ake yi ana yi ne domin talaka.
Hon. Gwajo-Gwajo ya ce a shirye suke da sauraren suka mai ma’ana, domin a cewarsa suka ba laifi ba ne, idan har zata sa abyi gyara wanda zai amfani al’umma baƙi ɗaya.
“Muna son ɗan adawa ya zo ya faɗi abinda yake ganin ba daidai bane, muna san haka, domin shi duk wanda ya ce gyara kayanka ai baya zama sauke mu raba” Cewarsai.
A cewar Hon. Yau Umar Gwajo-Gwajo abinda ba daidai ba shi ne, a kawo abu da babu shi, amma don gwamnati ta ce zata yi wani abu ɗan adawa ya ce ba daidai bane, za a tsaya a duba wannan abu a gani domin samun maslaha.
‘Yan adawa muna maraba da ku, muna gayyatar ku, ku zo a yi wannan gwamnati da ku, domin ta haka ne jihar Katsina zata kai wani matsayi da ba a tunani’ inji Gwajo-Gwajo.
Haka kuma ya yi kira ga ‘yan jarida da su bada ta su gudunmawa wajan ganin wannan gwamnati ta Malam Dikko Raɗɗa ta yi nasara, inda ya ce ‘yan jarida suna muhimmiyar rawar da za su taka wajan kawo gyara a tsarin dimokuraɗiyya.
Ya yi kira ga ‘Yan jarida da su ci gaba da aikinsu ta hanyar tuntuɓar gwamnati akan abinda ya shafe ta kai tsaye, inda ya yi alkawarin cewa kofa a buɗe take akan duk wani ƙarin haske daga ɓangaren gwamnati.
Kazalika ya bada tabbacin cewa wannan ofis ɗin shi, a shirye yake wajan ganin ya yi aiki da kowane ɓangare tunda ofis ne na siyasa, a cewarsa ofis ɗin yana da alaƙa da kowane ɓangare na gwamnatin jihar Katsina.