Ana sa ran, nan ba da jimawa ba kadan gamayyar ‘yan siyasar adawa a Nijeriya da suka narke a jam’iyyar ADC, don tunkarar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, za su bayyana yadda za a kasafta tsarin jagorancin jam’iyyar.
Har ila yau, manyan ‘yan siyasar sun amince ne da dunguma zuwa jam’iyyar ADC, wadda tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Dabid Mark ke jagoranta, bayan gaza cimma kafa wata sabuwar jam’iyya; sakamakon jan kafa wajen yi mata rijista da hukumar zaben kasar ke yi.
- INEC Ta Ayyana 16 Ga Agusta Don Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihohi 12
- Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar
Dantakarar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da na Labour Party, Peter Obi, na cikin jiga-jigan ‘yan adawar da suka shafe yinin ranar Talatar suna tattaunawa, inda kowane bangare ya gana da abokan tafiyarsa kafin cimma matsayar da aka samu.
Sauran sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na SDP da tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi na APC da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola na APC, duk a karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark na PDP.
Haka zalika, an tattauna ne a kan abubuwan da ake ganin za su zama ginshiki na sauran tafiyar da za a yi, a cewar Ibrahim Usaini Abdulkarim, wani na hannun daman Peter Obi, sannan kuma wanda ya halarci taron da aka gudanar a ranar Talatar.
Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba.
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada zumunta.
Matakin ‘yan adawar na shiga ADC, na zuwa ne bayan kasa cimma bukatarsu ta yi wa sabuwar kungiyar mai suna ‘All Democratic Alliance’ (ADA), rajista a matsayin jam’iyyar siyasa, sakamakon jan kafa da suka rika samu daga babbar hukmar zabe ta kasa (INEC).
Haka zalika, Atiku Abubakar da wasu manyan jam’iyar PDP, sun nemi ‘yan jam’iyyar da su hada hannu da su wajen shiga hadakar ta ADC, domin kalubalantar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027 mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp