‘Yan adawa sun siffanta mulkin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu na tsawon shekara daya a matsayin bai tsinana wa ‘yan Nijeriya da komi ba.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya bayyana cewa shekarar farko na mulkin Tinubu bai haifar da da mai ido ba, saboda bai aiwatar da wani tsari na a zo a gani ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitara a ranar Talata.
- Ina Kokarin Cika Alkawuran Da Na Dauka – Tinubu
- Sojojin Nijar Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Zamfara
A cewarsa, lokacin da aka rantsar da Tinubu ya lasa wa ‘yan Nijeriya zuma a baki na cewa zai farfado da tattalin arziki da samar da ayyukan yi da samar da tsaro da kawo karshen fatara a kasar nan.
Atiku ya ce lokacin da ‘yan Nijeriya suka ji kalamansa sai suka dauka zai kawo musu sauki a kan ukubar da suka sha na mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na tsawon shekara 8.
“Tinubu bai yi wani tsari kan sake farfado da tattalin arziki ba, sai dai ma ya kara dagula lamura.
“A watan Mayun 2023, ya cire tallafin man fetur, bayan wata daya kuma, babban bankin Nijeriya ya kaddamar da sabon tsari kan hada-hadar canjin kudaden waje na bai daya.
“Wadannan tsari sun yi matukar raunata tattalin arzikin kasar nan, wanda suka kara talauta ‘yan Nijeriya tun daga wannan lokaci har zuwa yau.”
A nasa bangaren, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya siffanta shekara daya na mulkin Tinubu a matsayin gazawa ta karshe.
Sowore idan shi malami ne zai rushe ajin da Tinubu yake da ya ba shi maki. Dan takarar shugaban kasan na AAC ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita.
“Idan ni malami ne ba zan taba bai wa Tinubu maki kan mulkinsa na shekara guda ba, ni zan ma rutse ajin ne saboda babu abin da za a iya ba shi na maki.
“Ina mai tabbatar da cewa wannan mulki na shekara guda ba mu karu da komi ba. An samu hauhawar farashin kayayyaki wanda ba a taba samu ba, rashin ayyukan yi ya kara kazanta, rashin tsaro ya kara ta’azzara a cikin shekara daya, sannan kuma gwamnati ta kasa biyan mafi karancin albashi.”
Su kuwa ‘yan majalisa na jam’iyyar LP sun bayyana cewa Tinubu bai cika alkawarin da ya yi wa ‘yan Nijeriya lokacin yakin neman zabe a tsawon mulkinsa na shekara daya ba.
Sun ce an samu karuwar rashin tsaro da matsin tattailin arziki a tsawon mulkin Tinubu na shekara guda.
‘Yan majalisar karkashin jagorancin Afam Ogene ya ce ‘yan Nijeriya za a tambaya ko Tinubu ya cika alkawarin da ya yi a cikin shekara guda.
Sun dai yi Kiara da Shugaba Tinubu da ya gaggauta rage wa ‘yan Nijeriya wahalhalun da suke fama da shi a halin yanzu, tare da tabbatar an samu wadataccen abinci da ruwan sha da kiwon lafiya da kuma ingantaccen ilimi.