Ana zargin wasu ‘yan bijilanti a garin Dabai da kashe wani malamin makarantar allo da ke karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Malam Musa Mai-Almajirai, ya kasance mashahurin malamin kur’ani a cikin al’umma, tare da daruruwan almajirai.
- Mayakan Taliban Sun Yi Arangama Da Masu Gadin Iyakar Iran
- Da Dumi-Dumi: ASUU Ta Tsawaita Yajin Aikinta Zuwa Makonni 4
An bayyana cewa an yi masa dukan tsiya har lahira a ofishin ‘yan bijilanti bayan wata mata ta zarge shi da satar yaro.
Ibrahim, dan malamin da ya rasu, ya shaida wa wakilinmu da safiyar ranar Litinin cewa, an kama kwamandan ‘yan bijilantin da laifin aikata kisan kai
“Yana wucewa sai ya ji wani jariri yana kuka a wajen wanj juji. Ya yanke shawarar daukar yaron, ana cikin haka sai wata mata ta daka masa tsawa tana kiransa da barawon yaro.” Inji Ibrahim.
“Kururuwar matar ta jawo hankalin ’yan bijilanti da sauran jama’ar unguwar da suka fara dukansa.
“Sun kai shi ofishin ‘yan bijilanti suka ci gaba da dukansa. Daga baya, ya fadi.
“Wasu mazauna garin sun gane shi daga baya kuma suka garzaya da shi asibiti, amma kafin a karasa asibiti rai ya yi halinsa.
“’Yan sanda sun kama kwamandan ‘yan bijilantin yankin, mai suna Munkaila, ana yi masa tambayoyi a caji ofis din Rigiyar Zaki,” in ji Ibrahim.
Ya ce an mika yaron da aka tsinta ga hakimim garin.
Ya kara da cewa “Al’amarin ya riga ya shafi ‘yan sanda, mun yi imanin cewa za su yi wa kowa adalci.”
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.