• Leadership Hausa
Tuesday, March 21, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bijilanti Sun Kashe Malamin Makarantar Allo A Kano

by Sadiq
8 months ago
in Al'ajabi
0
Jami’an Tsaro Sun Kashe Mahara 2 A Anambra, Sun Kwato Makamai 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ana zargin wasu ‘yan bijilanti a garin Dabai da kashe wani malamin makarantar allo da ke karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Malam Musa Mai-Almajirai, ya kasance mashahurin malamin kur’ani a cikin al’umma, tare da daruruwan almajirai.

  • Mayakan Taliban Sun Yi Arangama Da Masu Gadin Iyakar Iran
  • Da Dumi-Dumi: ASUU Ta Tsawaita Yajin Aikinta Zuwa Makonni 4

An bayyana cewa an yi masa dukan tsiya har lahira a ofishin ‘yan bijilanti bayan wata mata ta zarge shi da satar yaro.

Ibrahim, dan malamin da ya rasu, ya shaida wa wakilinmu da safiyar ranar Litinin cewa, an kama kwamandan ‘yan bijilantin da laifin aikata kisan kai

“Yana wucewa sai ya ji wani jariri yana kuka a wajen wanj juji. Ya yanke shawarar daukar yaron, ana cikin haka sai wata mata ta daka masa tsawa tana kiransa da barawon yaro.” Inji Ibrahim.

Labarai Masu Nasaba

Tarihin Mamayar Tattar II

Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)

“Kururuwar matar ta jawo hankalin ’yan bijilanti da sauran jama’ar unguwar da suka fara dukansa.

“Sun kai shi ofishin ‘yan bijilanti suka ci gaba da dukansa. Daga baya, ya fadi.

“Wasu mazauna garin sun gane shi daga baya kuma suka garzaya da shi asibiti, amma kafin a karasa asibiti rai ya yi halinsa.

“’Yan sanda sun kama kwamandan ‘yan bijilantin yankin, mai suna Munkaila, ana yi masa tambayoyi a caji ofis din Rigiyar Zaki,” in ji Ibrahim.

Ya ce an mika yaron da aka tsinta ga hakimim garin.

Ya kara da cewa “Al’amarin ya riga ya shafi ‘yan sanda, mun yi imanin cewa za su yi wa kowa adalci.”

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Tags: 'Yan Bijilanti'Yan SandaDabaiGwaleJaririkanoMalamin Makarantar AlloZargi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Mayakan Taliban Sun Yi Arangama Da Masu Gadin Iyakar Iran

Next Post

Ta Yaya Mamallakin Facebook Da WhatsApp Suke Samun Kudi?

Related

Tarihin Mamayar Tattar II
Al'ajabi

Tarihin Mamayar Tattar II

1 week ago
Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)
Al'ajabi

Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)

2 weeks ago
Zaben 2023: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC 3 A Taraba
Al'ajabi

Zaben 2023: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC 3 A Taraba

3 weeks ago
Mai Juna Biyu Ta Rasu A Rumfar Zabe A Jihar Zamfara
Al'ajabi

Mai Juna Biyu Ta Rasu A Rumfar Zabe A Jihar Zamfara

3 weeks ago
‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Kan Zargin Mallakar Kudaden Jabu A Jihar Kebbi
Al'ajabi

‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Kan Zargin Mallakar Kudaden Jabu A Jihar Kebbi

4 weeks ago
Fasto Ya Mutu A Kokarin Yin Azumin Kwana 40
Al'ajabi

Fasto Ya Mutu A Kokarin Yin Azumin Kwana 40

1 month ago
Next Post
Ta Yaya Mamallakin Facebook Da WhatsApp Suke Samun Kudi?

Ta Yaya Mamallakin Facebook Da WhatsApp Suke Samun Kudi?

LABARAI MASU NASABA

Jihar Zamfara: Dauda Lawal Dare Na Jam’iyyar PDP Ya Kayar Da Gwamna Matawalle Na APC

Jihar Zamfara: Dauda Lawal Dare Na Jam’iyyar PDP Ya Kayar Da Gwamna Matawalle Na APC

March 21, 2023
An Kaddamar Da Shirin Bidiyon “Bayanin Magabata Da Xi Jinping Ke So” Na 2 Da Harshen Rashanci 

An Kaddamar Da Shirin Bidiyon “Bayanin Magabata Da Xi Jinping Ke So” Na 2 Da Harshen Rashanci 

March 20, 2023
Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha Vladimir Putin

Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Rasha Vladimir Putin

March 20, 2023
Ramadan: Shehu Isma’ila Mai Diwani Ya Buɗe Tafsirin Alƙur’ani A Kaduna

Ramadan: Shehu Isma’ila Mai Diwani Ya Buɗe Tafsirin Alƙur’ani A Kaduna

March 20, 2023
Firaministan Kasar Djibouti Ya Mikawa Tawagar Jiyya Ta Kasar Sin Lambar Yabo

Firaministan Kasar Djibouti Ya Mikawa Tawagar Jiyya Ta Kasar Sin Lambar Yabo

March 20, 2023
Da Dumi-duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Ondo

An Sace Baturen Zabe Akan Hanyarsa Ta Zuwa Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe A Zamfara

March 20, 2023
Dangantakar Sin Da Rasha Ta Bayyana “Hanyar Da Ta Dace Ta Cudanya Tsakanin Kasa Da Kasa”

Dangantakar Sin Da Rasha Ta Bayyana “Hanyar Da Ta Dace Ta Cudanya Tsakanin Kasa Da Kasa”

March 20, 2023
Gwamna Zulum Ya Sake Lashe Zaben Gwamna A Jihar Borno

Gwamna Zulum Ya Sake Lashe Zaben Gwamna A Jihar Borno

March 20, 2023
An Kashe ‘Yansanda 2, Da Dama Sun Samu Raunuka A Wata Arangama Da Sojoji A Taraba

An Kashe ‘Yansanda 2, Da Dama Sun Samu Raunuka A Wata Arangama Da Sojoji A Taraba

March 20, 2023
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Sauran Kasashen Yammacin Duniya Da Su Gaggauta Dage Takunkumin Kan Bangare Daya

Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Sauran Kasashen Yammacin Duniya Da Su Gaggauta Dage Takunkumin Kan Bangare Daya

March 20, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.