‘Yan Bijilanti da ke yin aikin sintiri a karamar hukumar Lere tare da hadin kan matasa a yankin sun kashe wata mata da ake zargin mai garkuwa da mutane ce, sun kuma yi nasarar cafke barayin mutane 12 a yayin kai sumamen.
‘Yan Bijilantin sun samu wannan nasarar ce a ranar Talata bayan sun kai farmaki a maboyar masu garkuwar da ke Garun Kurama a shiyyar Mariri.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa 17 A Filato
- Kotu Ta Amince Da Bayar Da Belin Wanda Ya Yi Garkuwa Da Yayarsa A Zariya
Wani jagora a yankin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, ‘yan Bindigar sun jima suna addabar mazauna yankin.
Shi ma wani dan Bijilanti da bai son a bayyana sunansa ya ce, an kashe matar mai garkuwa da mutane ne a wani samame da ‘yan Bijilantin suka kai da misalin karfe 3 na daren ranar ta Talata.
A cewarsa, “Mun cafke wadanda ake zargin masu garkuwar da mutane ne su 13 a maboyarsu”.
Ya sanar da cewa, “Mun kuma lalata sansaninsu, inda a nan take, muka kashe wata mace mai garkuwa da mutane da wadanda aka cafke aka mika su ga ‘yan sanda.
Sai dai, Kakakin Rundunar ‘yan sanda na jihar DSP Mohammed Jalige, bai fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.