Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya ce ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a Nijeriya sun fi sojojin ƙasar makamai da kayan aiki.
Lawal ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, inda ya tattauna kan matsalar tsaro a ƙasar.
- Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa
- Xi Ya Taya Ouattara Murnar Sake Lashe Zaben Shugaban Cote D’Ivoire
A cewarsa, “Abin mamaki ne ganin cewa waɗannan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda suna da makamai sama da na sojojin Nijeriya. Kayayyakin da suke da su suna da yawa sosai, hakan na nuna cewa akwai wanda ke ɗaukar nauyinsu.”
Ya ƙara da cewa, “Shin ba ya baku mamaki cewa wata ƙungiya ko wasu mutane na tallafa musu? Domin kayan da suke da su sun yi yawa sosai. Abin da kawai bai rage musu ba shi ne su fara tashi da jiragen sama suna aikata ta’addanci.”
Babachir Lawal ya yi kira ga gwamnati ta ƙara himma wajen gano tushen kuɗaɗen da ke tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.














