Wani mummunan rikici da ya barke a tsakanin yan bindiga a kauyen Kewaye da ke karamar hukumar mulkin Anka a Jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 30 daga cikin su, wasu kuma sun samu munanan raunuka.
Rahotanni sun bayyana cewa, ƴan bindigar ne suka koro shanu zuwa kauyen inda a wajen rabon shanun sai aka bai wa wasu yan kadan wasu aka basu masu yawa, wanda hakan ya sa fada ya barke a tsakanin su, suka dinga musayar wuta, kuma nan take aka kashe mutane fiye da talatin (30) sannan fiye da 20 da sun jikkata.
- Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaryata Ware Biliyan 19 Don Sanya Wa Lawal Kayan Girki
- Sabon Jakadan Sin Ya Isa Najeriya Domin Kama Aiki
Fadan ya barke ne tsakanin yaran wasu manyan yan bindigar yankin, wato yaran Kachalla Halilu da yaran Bello Kaura, wadanda duka shahararrun ƴan bindiga ne a yankin.
Kawo yanzu dai, rundunar ƴansandan jihar ba ta ce komai ba a kan lamarin.