‘Yan bindiga na neman Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa kafin su sako yara da matan da suka yi garkuwa da su a kauyen Wanzamai na Jihar Zamfara.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa a ranar Alhamis ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane kusan 100 a gonakinsu a jihohin Zamfara da Katsina.
Wata majiya ta bayyana cewa a kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, an yi garkuwa da yara kusan 80.
An yi garkuwa da wasu mutane fiye da 20 daga kauyukan da ke makwabtaka da su.
Ya kuma yi bayanin cewa masu garkuwa da mutanen sun kira wasu daga cikin iyalan wadanda abin ya shafa, inda suka bukaci a biya su miliyan 60 kafin su sako yaran.
Ya kara da cewa, “An fara tattaunawa sosai kuma masu garkuwa da mutanen sun rage kudin fansar zuwa Naira miliyan 30. Sun bukaci iyalan wadanda abin ya shafa su je su tara kudin.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Muhammad Shehu, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Kolo Yusuf ya tabbatar wa jama’a musamman iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, cewa rundunar tare da hadin gwiwar sojoji da ‘yan banga suna kokarin aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.