Wasu ‘yan bindiga sanye da hijabi sun kai hari ofishin ‘yansanda, tare da kashe dan sanda guda daya a kauyen Saki Jiki da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abubakar Aliyu Sadiq, a wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wani dan sanda ya samu rauni a harin, ba ya ga wani daya da ya rasu.
- Nijeriya Na Fatan Samun Karin Masu Zuba Jari A Taron Kasuwanci Na Duniya
- Matsafa Sun Sare Kan Budurwa A Adamawa
Sadiq, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis, kuma tuni ‘yansanda suka dakile harin.
Ya ce, “A jiya (Alhamis) da misalin karfe 8 na dare wasu ‘yan bindiga sanye hijabi, suka farmaki ofishin ‘yansanda da ke kauyen Saki Jiki a Karamar Hukumar Batsari.
“Jami’an sun yi artabu da su kuma sun yi nasarar dakile harin. Sai dai jami’i daya ya rasa ransa sannan wani ya samu rauni sakamakon harin.
“Za a sanar da ci gaban da aka samu nan gaba.”
Karamar hukumar Batsari dai na fuskantar sabbin hare-haren ‘yan bindiga a baya-bayan nan.
A cikin mako guda, ‘yan bindiga sun kai hari biyu a yankin.