Wasu ‘yan bindiga dadi a ranar Asabar sun banka wuta ga ginin babban kotun jihar Imo da ke matsuguni a Orlu, lamarin da ya janyo wasu gine-ginen kotun konewa da kuma wasu muhimman bayanai da takardun da suka kone kurmus.Â
Lamarin na zuwa ne kasa da ‘yan kwanaki da wasu ‘yan bindigan suka kai hari Shalkwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke Owerri.
An nakalto cewa babban kotun na hade da dakunan shari’a na babban kotun da kuma na kotunan majistare.
Wani ma’aikacin kotun da ya yi magana da ‘yan jarida bisa sharadin za a boye sunansa ya ce dukkanin fiyel-fayel sun kone kurmus a sakamakon wannan wutar.
Babban kotun Orlu a jihar Imo dai na kusa-kusa da wani shingen binciken jami’an tsaro da kuma Shalkwatar shiyya ta hukumar ‘yansanda.
A shekarar 2018, an taba rushe kotun. A ranar 1 ga watan Disamba kuma aka banka wa ofishin INEC da ke Orlu wuta dukka da irin wannan sigar.
Shugaban kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen Orlu, Barnabas Munonye, ya tabbatar da faruwar wannan lamarkn tare da misalta hakan a matsayin abin kaito da tir.
Kakakin ‘yansandan jihar Imo, CSP Mike Abattam, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tunin kuma suka kaddamar da bincike kan wannan lamarin.