‘Yan sanda uku sun mutu lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi wa tawagar jami’an tsaron gwamnan Ifeanyi Okowa na jihar Delta kwanton bauna.
Lamarin ya faru ranar Juma’ar nan da misalin karfe 1:30 na rana.
- Atiku Da Okowa Sun Janye Daga Taron Ganawa Da ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
- Okowa Ya Karbi Wadanda Suka Nemi Takarar Gwamnan APC Uku Da Suka Koma PDP A Sakkwato
Okowa shi ne mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa ‘yan bindigar sun kai wa tawagar jami’an tsaro hari wadanda suka hada da ‘yan sanda hudu a unguwar Ihiala, da ke karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.
Sai dai an ce wai ‘yan bindigar sun sako daya daga cikin jami’an da ba ya cikin kakin ‘yan sanda a yayin harin.
Wasu majiyoyi sun ce jami’an na kan hanyar zuwa jihar Abia ne, inda Okowa zai je don ganawa da wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar gabanin zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kawo yanzu dai ba a bayyana ko Okowa na tafiya tare da jami’an ba a yayin kai harin ba.
Jami’an da aka kashe sun hada da Celestine Nwadiokwu da Jude Obuh da kuma Lucky Aleh.
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga a safiyar ranar Asabar, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ikenga, ya ce wadanda harin ya rutsa da su jami’an su ne da ke aiki a sashin kula da bama-bamai na rundunar ‘yan sandan jihar Delta kuma suna bakin aikin lamarin ya faru.
Kakakin ‘yan sandan ya ce rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta gano gawarwakin jami’an uku da aka kashe bayan samun labarin kai harin.