Majalisar dokokin Jihar Neja, ta damu kan yadda ‘yan bindiga suka fara mamaye dajin da ake horar da sojojin Nijeriya da ke karamar hukumar Kontagora.
A wani zama da majalisar ta gudanar a ranar Talata, dan majalisar mai wakiltar Kontagora ta 2, Hon. Abdullahi Isah, ya ce yanzu ‘yan bindiga sun kwace wa sojojin Nijeriya wannan daji kuma a nan ne suke kai mutanen da suka yi garkuwa da su domin neman kudin fansa.
- Sin Ta Yi Kira Da a Yi Hakuri Da Juna Tare Da Nuna Adawa Da Keta Zaman Lafiya a Yankin Gabas Ta Tsakiya
- Sin Za Ta Harba Kumbon “Shenzhou-19” Mai Daukar ’Yan Sama Jannati 3
Majalisar ta bukaci gwamnatin jihar da rundunar soji da su yi duk mai yiwuwa domin kwato daji daga hannun ‘yan bindigar.
Dan majalisa mak wakiltar Kontagora, Hon. Sani Umar Blak, ya ce lamarin yana da matukar tayar da hankali.
Shi ma shugaban karamar hukumar Kontagora, Hon Shehu s. Pawa, ya tabbatar da cewa yanzu ‘yan bindiga ne ke rike da dajin ba sojojin Nijeriya ba.
Sai dai a lokacin da na tuntubi mai magana da yawun rundunar sojin da ke Barikin sojojin na Kontagora, Kyaftin Iliya Bawa, ya karyata labarin.
Ya ce dakarun rundunar kullum suna shiga cikin dajin domin yin atisaye.