Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani Lauya, Barista Benedict Azza a garin Gusau, babban birnin Jihar Zamfara a ranar Alhamis.
A wata sanarwar da shugaban kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen Gusau (NBA), Junaidu Abubakar ya fitar, ya ce bisa bayanan da suka samu ‘yan bindigan sun kai hari wa Lauyan ne a kokarinsu na yin garkuwa da shi.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 69 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Bauchi
- Yadda Matuka Jirgi Suka Shantake Da Bacci A Lokacin Sauka
“Jiya wajajen karfe 2230hrs, a lokacin ina gidana, na amshi kiran waya daban-daban har guda uku daga abokan aikinmu su na shaida min cewa wasu ‘yan bindigan da ba san ko su waye ba sun harbe B. T. Azza Esq har lahira kuma gangar jikinsa an yasar a kan hanya kusa da ofishin FRSC da ke Gusau.
Shugaban na NBA ya yi zargin cewa wasu ‘yan bindiga su biyu a kan Babur ne suka kashe Lauyan a lokacin da suka yi kokarin yin garkuwa da shi a gidansa da ke layin Saminaka da ke kusa da ofishin FRSC na Gusau yayin da shi Kuma Lauyan ya shiga motarsa da yunkurin tserewa ne suka iya cimma masa.
Sanarwar ta kara da cewa makwabtan Barista Azza sun ji karar harbe-harbe a yankin daga baya suka ji karar hatsarin mota, “Da suka je wajen sun ga motarsa a bude an ja kasa shi yana kwance na ta zubar da jini.”
Ya kara da cewa sau uku masu bindigar suka harbi Lauyan. Ya yi kira ga jami’an tsaro da su binciko wadanda suka kashe Lauyan tare da hukunta su.