ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 20, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Hallaka ‘Yan Sa-kai Sama Da 70 A Filato

by Sadiq
1 year ago
Filato

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sa-kai sama da 70 a ƙauyukan Kukawa da Bunyun da ke Ƙaramar Hukumar Kanam a Jihar Filato.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Litinin, lokacin da ɗaruruwan ‘yan sa-kai daga ƙaramar hukumar Wase ke kan hanyarsu ta zuwa daji inda aka ce ‘yan bindiga na ɓuya, amma sai aka yi musu kwanton-ɓauna a hanyar.

  • ADC: Tinubu Na Yunƙurin Raba Kawunan Masu Haɗaka Kafin Zaɓen 2027
  • Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima

Shugaban ‘yan sa-kai na Kukawa, Aliyu Baffa, ya ce ‘yan sa-kai sama 70 aka kashe, kuma akwai yiwuwar a gano wasu gawarwakinsu a daji.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana cewa kwanton-ɓaunar ta faru ne kusan kilomita ɗaya daga garin Kukawa, kusa da dajin da ake kira Madam Forest, wanda ke iyaka da Jihohin Bauchi da Taraba.

Baffa ya ƙara da cewa an gano gawarwakin wasu a gonaki.

LABARAI MASU NASABA

An Ceto Mutane 17 da Aka Yi Garkuwa da Su Bayan Musayar Wuta a Wani Daji a Kogi

Ƴan Gudun Hijira Sun Buƙaci A Kafa Masu Akwatin Zaɓe, Sun Bijire Tafiya Gwoza Zaɓe

“Mun riga mun binne sama da mutum 60 a Kukawa kaɗai,” in ji shi.

“Wadanda suka tsira sun ce ‘yan bindigar sun fi ƙarfinsu.”

Wani mazaunin ƙauyen Bunyun da ke gundumar Nyalun a ƙaramar hukumar Wase, Musa Ibrahim, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyensu, inda suka kashe ‘yan sa-kai 10 da ke tsaron yankin.

Musa ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun ƙone gidaje da dama a ƙauyen.

MASU ALAKA

An Ceto Mutane 17 da Aka Yi Garkuwa da Su Bayan Musayar Wuta a Wani Daji a Kogi
Manyan Labarai

An Ceto Mutane 17 da Aka Yi Garkuwa da Su Bayan Musayar Wuta a Wani Daji a Kogi

November 19, 2026
Ƴan Gudun Hijira Sun Buƙaci A Kafa Masu Akwatin Zaɓe, Sun Bijire Tafiya Gwoza Zaɓe
Manyan Labarai

Ƴan Gudun Hijira Sun Buƙaci A Kafa Masu Akwatin Zaɓe, Sun Bijire Tafiya Gwoza Zaɓe

November 19, 2026
Kashinku Ya Bushe: Sojoji Sun Lashi Takobin Kawo Ƙarshen ‘Yan Ta’adda A Zamfara Da Katsina 
Manyan Labarai

Hare-Hare Ta Sama Sun Hallaka Mayaƙan ISWAP 21 A Jihar Borno

November 19, 2026
Next Post
ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Nijeriya

ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Masana Kan Harkokin Tattalin Arziki Da Kasuwanci Na APEC A Shenzhen

An Gudanar Da Taron Masana Kan Harkokin Tattalin Arziki Da Kasuwanci Na APEC A Shenzhen

November 18, 2026
Zaɓen 2027: INEC Ta Ci Gaba Da Ayyana Sunan Atiku A Matsayin Ɗan Takarar ADC Duk Da Rikicin Shugabanci

Zaɓen 2027: INEC Ta Ci Gaba Da Ayyana Sunan Atiku A Matsayin Ɗan Takarar ADC Duk Da Rikicin Shugabanci

November 18, 2026
Xi Ya Ce Alakar Sin Da Rasha Na Kawo Kwanciyar Hankali Da Tabbaci Ga Duniya Mai Cike Da Rudani

Xi Ya Ce Alakar Sin Da Rasha Na Kawo Kwanciyar Hankali Da Tabbaci Ga Duniya Mai Cike Da Rudani

November 18, 2026
Majalisar Dattawa Ta Kammala Shirin Kafa ’Yansandan Jihohi, Ta Nemi Amincewar Tinubu

Majalisar Dattawa Ta Kammala Shirin Kafa ’Yansandan Jihohi, Ta Nemi Amincewar Tinubu

November 18, 2026
Xi Ya Tarbi Trump A Filin Jiragen Sama Na Shenzhen

Xi Ya Tarbi Trump A Filin Jiragen Sama Na Shenzhen

November 18, 2026
Matashi Ya Rasu Bayan Ya Faɗa Cikin Kududdufi A Kano

Kano: An Kama Masu Karɓar Haraji Ba Bisa Ƙa’ida Ba

November 18, 2026
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohowar Shugaban Kotun Gargajiya A Benue

Kotu A Kano Ta Tsare Malamin Jami’a Kan Alaƙanta Kamfanin Rufaida Yoghurt Da Malami

November 18, 2026
Taron Shugabannin Kamfanoni Na APEC Na Shekarar 2026 Ya Fitar Da “Shawarar Shenzhen”

Taron Shugabannin Kamfanoni Na APEC Na Shekarar 2026 Ya Fitar Da “Shawarar Shenzhen”

November 18, 2026
Xi Ya Shirya Liyafar Maraba Ga Bakin Da Suke Halartar Taron APEC

Xi Ya Shirya Liyafar Maraba Ga Bakin Da Suke Halartar Taron APEC

November 18, 2026
NDLEA Ta Kama Tabar Wiwi Buhu 116 A Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane Takwas Da Ke Safarar Hodar Iblis Daga Legas Zuwa Turai

November 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.