Wasu ‘yan bindiga da suka kai kimanin 20 a daren Juma’a da misalin karfe 11:30 na dare sun kai farmaki rukunin gidaje na Grow Homes da ke Kuchibiyi a yankin Kubwa a babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna unguwar kimanin tara da suka hada da mata da kananan yara.
Wani mazaunin unguwar da ya bayyana sunansa da Hassan, ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutanen ne daga wasu gidaje guda biyu kuma lamarin ya haifar da firgici a yankin.
- Zulum Ya Ziyarci Iyalan Masuntan Da Boko Haram Ta Hallaka A Borno
- Mutum 2 Sun Shiga Hannu Kan Yi Wa Mace Kurma Fyade A Jihar Nasarawa
“A jiya da misalin karfe 11:30 na dare wasu ‘yan bindiga da yawa sun zo domin kai farmaki a rukunin gidaje na Grow Homes da ke Kuchibiyi. Mun ji karar harbe-harbe, an shiga firgici a daukacin yankin.
“Da safiyar yau, mun je gidan, muka samu labarin cewa ‘yan bindigar sun kai kimanin 20. Sun tashi daga wani gida zuwa wancan suna korar mazauna yankin. Sun kuma yi garkuwa da akalla mutane tara da suka hada da yara da mata daga wasu gidaje biyu.
“Sun tsere ne cikin daji wanda ya danganta al’ummar kauyen Paze. Tun da safe ‘yansanda da jami’an tsaro sun fara bincike a daji don ganin ko za su iya kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, yayin da ta ke tabbatar da afkuwar lamarin, ta ce ‘yansanda da jami’an tsaro na kokarin ceto mutane.
“Bayan samun kiran gaggawa nan take muka tura mutanenmu wurin. Sai dai wadanda ake zargin sun tsere zuwa daji.
“Rundunar ‘yansanda da jami’an tsaro na ci gaba da bincike a yankin domin ganin an ceto su ba tare da wani rauni ba,” in ji ta.
Ta kuma bukaci mazauna yankin da kada su firgita, inda ta yi kira gare su da su taimaka wa ‘yansanda da sahihan bayanan da za su kai ga cafke maharan.
“Muna kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da bayanai masu amfani da za su iya kai ga cafke wadannan masu laifin cikin gaggawa,” in ji SP Adeh.