Wasu mahara sun kai wa zababben dan majalisar da ke wakiltar Gbemacha, wanda aka fi sani da mazabar Gboko ta yamma a majalisar dokokin jihar Benue na jam’iyyar APC, Aondona Dajoh, hari.
Dajoh, wanda aka kaiwa hari da misalin karfe 10 na daren ranar Alhamis a garin Gboko tare da kone motarsa da maharan suka yi, sai dai ya tsallake rijiya da baya.
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Adeleke A Matsayin Gwamnan Osun
- EFCC Ta Shirya Tsab Don Bincikar Gwamnoni 2 Masu Barin Gado Kan Zargin Badakalar Kudade
Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Binuwe, Catherine Anene, wacce aka tuntube ta ta wayar tarho, ta tabbatar da harin da aka kai wa dan majalisar.
“Duk da cewa ya tsira da ransa, motarsa ta kone,” in ji kakakin ‘yan sandan.
Wakilinmu ya rawaito cewa, cikin makusantan Dajoh, wanda ya so a sakaya sunansa ya ce, dan majalisar ya zauna da abokinsa ranar Alhamis bayan ganawarsa da dattawan Gbemacha a gidansa daga bisani dukkansu suka ta fi sabgoginsu.
Ya ce, “A kan hanyarsa ta dawowa daga Adekaa, da misalin karfe 10 na dare ya hangi wata mota ta madubi tana tuki a bayansa, bai ji dadin yadda motar ta zo ba kamar tana son ta tare shi, sai ya kara saurinsa.
“Nan da nan suka lura ya kara gudunsa, sai motar ta fara hasko shi ta baya, sai ya sake kara yawan gudunsa da gudu ya nufi wani wuri inda ya ga mutane da dama a kusa da titin asibitin Gyado ya ajiye motarsa ya tsallake shingen da ke kusa da shi don tsira da ransa.
“Saboda haka da motar ta isa inda ya ajiye motarsa da sauri suka sauko suka tare motar suka lura cewa babu kowa a cikin motar, sai suka kona motar suka gudu.” Inji shi.