Rundunar ‘Yan sandan jihar Edo ta bayyana cewa wasu da ake zaton makiyaya ne sun yi garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance yawansu ba da ke dakon shiga jirgin kasa daga Igueben ta karamar hukumar Igueben a jihar, zuwa Warri a jihar Delta.
Cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai, Kakakin Rundunar, Chidi Nwabuzor, ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Asabar.
- ‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa 3, Sun Ceto Wani Yaro Dan Wata 13 A Edo
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 32 Daga Masu Garkuwa
A cewar sanarwar, wadanda ake zargin makiyaya ne dauke da bindigu kirar AK-47, sun kutsa kai cikin tashar jirgin inda suka yi ta harbin iska, kafin daga bisani su yi awon-gaba da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba.
Sanarwar ta kara da cewa, wasu daga cikin fasinjojin aun samu raunuka sakamakon harbin bindiga.
Rundunar ‘Yansandan ta bayyana cewa, tana kokarin ganin an kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su tare da kamo masu laifin.