Rundunar ‘yansandan jihar Edo ta samu nasarar ceto mutum talatin da biyu daga hannun masu garkuwa da aka kama a kan hanyar Benin zuwa Agbor a makon da ya gabata.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Jennifer Iwegbu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Jami’in ya ce, “Rundunar ‘yansandan jihar Edo da taimakon ofishin ‘yansanda na Uronigbe, da ke karamar hukumar Orhihonwon sun samu nasarar kubutar da yara 32 da kuma wasu manya guda biyu a kan hanyar Benin zuwa Agbor Edpress da masu garkuwa suka kama.
“Bayan samun wani sahihin labara daga wasu mutanen gari, cewa an ga wasu mutane wadanda ake zaton masu garkuwa ne, sun fito daga daji sun bi hanyar Agbor zuwa Uronigbe zuwa Obiaruku sun shida wata mota kirar bos mai lamba DT513B2, sun bi hanyar Warri, wanda a kan hanya suka waske suka shiga daji”.
“Bayan samun wannan bayani sai ‘yansandan tare da hadin gwiwar sojoji da kuan ‘yan sintiri, suka garzaya, suka bi sawunsu”.
“Gamayyar jami’an tsaron, suka shiga dajin da maboyar masu garkuwan take, inda suka sanu nasarar kubutar da yara talatin da biyu da kuma manya guda biyu, su kuma ‘yan bindigar suka ranta a na kare, sai dai ba a ga mutum biyar ba, daga cikin wadanda masu garkuwar suka kai dajin.”